Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Fit 14:11-23 Littafi Mai Tsarki (HAU)

11. Suka ce wa Musa, “Donin ba makabarta a Masar, shi ya sa ka fito da mu, mu mutu a jeji? Me ke nan ka yi mana da ka fito da mu daga Masar?

12. Ashe, ba abin da muka faɗa maka tun a Masar ke nan ba cewa, ‘Ka rabu da mu, mu bauta wa Masarawa’? Gama gwamma mu bauta wa Masarawa da mu mutu a jeji.”

13. Sai Musa ya ce wa jama'a, “Kada ku tsorata, ku tsaya cik, ku ga ceton Ubangiji, wanda zai yi muku yau, gama Masarawan nan da kuke gani yau, ba za ku ƙara ganinsu ba faufau.

14. Ubangiji zai yi yaƙi dominku, sai dai ku tsaya kurum!”

15. Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Me ya sa kake yi mini kuka? Faɗa wa Isra'ilawa su ci gaba.

16. Ɗaga sandanka, ka miƙa hannunka a bisa bahar, ka raba shi, domin Isra'ilawa su taka busasshiyar ƙasa cikin bahar, su haye.

17. Ni kuwa zan taurare zukatan Masarawa domin su bi su. Ta haka zan ci nasara bisa Fir'auna da rundunansa, da karusansa, da mahayan dawakansa.

18. Masarawa kuwa za su sani ni ne Ubangiji, sa'ad da na sami nasara bisa kan Fir'auna, da karusansa, da mahayan dawakansa.”

19. Mala'ikan Allah kuwa wanda yake tafiya a gaban rundunar Isra'ila ya tashi ya koma bayansu, haka kuma al'amudin girgijen ya tashi daga gabansu ya tsaya a bayansu.

20. Ya shiga tsakanin sansanin Masarawa da zangon Isra'ilawa. Girgije mai duhu na tsakaninsu, amma ya haskaka wajen Isra'ilawa har gari ya waye, ba wanda ya kusaci wani.

21. Da Musa ya miƙa hannunsa bisa bahar, sai Ubangiji ya sa iskar gabas mai ƙarfi ta tsaga bahar, ta tura ta baya, ta yi ta hurawa dukan dare har bahar ta bushe, ruwan kuwa ya dāre.

22. Isra'ilawa kuwa suka bi ta tsakiyar bahar, a busasshiyar ƙasa. Ruwan ya zama musu katanga dama da hagu.

23. Masarawa kuwa suka bi su har tsakiyar bahar, da dawakan Fir'auna duka, da karusansa, da mahayan dawakansa.

Karanta cikakken babi Fit 14