Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Far 50:1-10 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Yusufu kuwa ya fāɗa a kan mahaifinsa, ya yi kuka a kansa, ya sumbace shi.

2. Sai Yusufu ya umarci barorinsa masu magani, su shafe gawar mahaifinsa da maganin hana ruɓa. Saboda haka masu maganin suka shafe Isra'ila da maganin hana ruɓa.

3. Suka ɗauki kwana arba'in cif suna yin wannan, gama kwanakin da ake bukata ke nan don shafewa da maganin hana ruɓa. Masarawa kuwa suka yi masa makoki na kwana saba'in.

4. Sa'ad da kwanakin makokin suka wuce, Yusufu ya yi magana da iyalin gidan Fir'auna, ya ce, “Idan fa yanzu na sami tagomashi a wurinku, ku yi magana, ina roƙonku a gaban Fir'auna, ku ce masa,

5. ‘Sa'ad da mahaifina yake bakin mutuwa, ya sa ni in yi masa alkawari, cewa zan binne shi a kabarin da ya haƙa wa kansa a ƙasar Kan'ana.’ Don haka in ya yarda ya bar ni in je in binne mahaifina, sa'an nan in komo.”

6. Fir'auna ya amsa, ya ce, “Ka haura ka binne mahaifinka, kamar yadda ya rantsar da kai.”

7. Saboda haka, Yusufu ya haura ya binne mahaifinsa, tare da shi kuma dukan barorin Fir'auna suka haura, da dattawan gidan Fir'auna, da dukan dattawan ƙasar Masar,

8. da kuma dukan iyalin gidan Yusufu, da 'yan'uwansa, da iyalin gidan mahaifinsa. Sai 'yan ƙananansu, da garkunan awaki da na tumaki, da garkunan shanunsu, aka bari a ƙasar Goshen.

9. Da karusai da mahayan dawakai kuma suka tafi tare da shi. Babbar ƙungiya ce ƙwarai.

10. Sa'ad da suka kai farfajiyar masussukar Atad, wanda yake wajen Urdun, a nan ne fa suka yi makoki, da babban makoki da baƙin ciki mai zafi. Aka kuwa yi kwana bakwai ana makokin mahaifinsa.

Karanta cikakken babi Far 50