Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Far 46:5-20 Littafi Mai Tsarki (HAU)

5. Sai Yakubu ya tashi daga Biyer-sheba, 'ya'yan Isra'ila maza kuwa suka ɗauki mahaifinsu Yakubu, da 'yan ƙananansu da matansu a cikin kekunan shanun da Fir'auna ya aika a ɗauko su.

6. Suka kuma kora shanunsu, suka ɗauki kayayyakinsu waɗanda suka samu a ƙasar Kan'ana, suka iso Masar, Yakubu da zuriyarsa duka,

7. 'ya'yansa maza da jikokinsa maza tare da shi, 'ya'yansa mata, da jikokinsa mata, ya kawo zuriyarsa dukka zuwa ƙasar Masar.

8. Waɗannan su ne sunayen 'ya'ya maza na Isra'ila, wato Yakubu, waɗanda suka iso Masar. Ra'ubainu, ɗan farin Yakubu.

9. 'Ya'yan Ra'ubainu, maza kuwa, su ne Hanok, da Fallu, da Hesruna, da Karmi.

10. 'Ya'yan Saminu, maza, su ne Yemuwel, da Yamin, da Ohad, da Yakin, da Zohar, da Shawul ɗan wata Bakan'aniya.

11. 'Ya'yan Lawi, maza, su ne Gershon, da Kohat, da Merari.

12. 'Ya'yan Yahuza, maza, su ne Er, da Onan, da Shela, da Feresa, da Zera, (amma Er da Onan suka rasu a ƙasar Kan'ana). 'Ya'yan Feresa, maza kuwa, su ne Hesruna da Hamul.

13. 'Ya'yan Issaka, maza, su ne Tola, da Fuwa, da Yashub, da Shimron.

14. 'Ya'yan Zabaluna, maza, su ne Sered, da Elon, da Yaleyel,

15. (waɗannan su ne 'ya'yan Lai'atu, maza, waɗanda ta haifa wa Yakubu cikin Fadan-aram, da 'ya tasa kuma Dinatu, 'ya'yansa mata da maza duka, mutum talatin da uku ne).

16. 'Ya'yan Gad, maza, su ne Zifiyon, da Haggi, da Shuni, da Ezbon, da Eri, da Arodi, da Areli.

17. 'Ya'yan Ashiru, maza, su ne Yimna, da Yishuwa, da Yishwi, da Beriya, da Sera, 'yar'uwarsu. 'Ya'yan Beriya, maza kuma, su ne Eber da Malkiyel.

18. Waɗannan su goma sha shida, su ne zuriyar Yakubu, maza, na wajen Zilfa, wadda Laban ya bai wa Lai'atu, 'yarsa.

19. 'Ya'ya maza, na Rahila, matar Yakubu, su ne Yusufu da Biliyaminu.

20. Asenat 'yar Fotifera, firist na On, ta haifa wa Yusufu Manassa da Ifraimu a ƙasar Masar.

Karanta cikakken babi Far 46