Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Far 45:14-25 Littafi Mai Tsarki (HAU)

14. Sai Yusufu ya rungumi ɗan'uwansa Biliyaminu ya yi ta kuka, Biliyaminu ma ya yi kuka a bisa kafaɗun Yusufu.

15. Ya sumbaci 'yan'uwansa duka, ya yi kuka bisansu, bayan wannan sai 'yan'uwansa suka yi taɗi da shi.

16. Sa'ad da labari ya kai gidan Fir'auna cewa, “'Yan'uwan Yusufu sun zo,” abin ya yi wa Fir'auna da fādawansa daɗi ƙwarai.

17. Sai Fir'auna ya ce wa Yusufu, “Ka faɗa wa 'yan'uwanka su yi wannan, ‘Ku yi wa dabbobinku laftu ku koma a ƙasar Kan'ana.

18. Ku ɗauko mahaifinku da iyalanku, ku zo wurina, ni kuwa zan ba ku yankin ƙasa mafificiya a Masar, za ku ci moriyar ƙasar.’

19. Ka kuma umarce su ka ce, ‘Ku ɗauki kekunan shanu daga ƙasar Masar domin 'yan ƙanananku da matanku, ku ɗauko mahaifinku, ku zo.

20. Kada ku damu da kayayyakinku, gama abin da yake mafi kyau duka a ƙasar Masar naku ne.’ ”

21. Haka kuwa 'ya'yan Isra'ila suka yi. Yusufu kuma ya ba su kekunan shanu bisa ga umarnin Fir'auna, ya ba su guzuri don hanya.

22. Ga kowane ɗayansu ya ba da rigar ado, amma ga Biliyaminu ya ba da azurfa ɗari uku, da rigunan ado biyar.

23. Ga mahaifinsa kuwa ya aika da jakai goma ɗauke da kyawawan abubuwa na Masar, da jakai mata goma ɗauke da tsaba, da kuma abinci da guzurin hanya saboda mahaifinsa.

24. Ya sallami 'yan'uwansa. Da suna shirin tashi, sai ya ce musu, “Kada ku yi faɗa a hanya.”

25. Suka haura daga Masar, suka zo ƙasar Kan'ana zuwa wurin Yakubu mahaifinsu.

Karanta cikakken babi Far 45