Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Far 44:13-29 Littafi Mai Tsarki (HAU)

13. Suka kyakkece rigunansu, kowannensu kuwa ya yi wa jakinsa labtu suka koma birnin.

14. Sa'ad da Yahuza da 'yan'uwansa suka zo gidan Yusufu, suka iske yana nan har yanzu, sai suka fāɗi ƙasa a gabansa.

15. Yusufu ya ce musu, “Wane abu ke nan kuka aikata? Ba ku sani ba, mutum kamata yakan yi istihara?”

16. Sai Yahuza ya amsa, “Me za mu ce wa shugabana? Wace magana za mu yi? Ko kuwa, ta yaya za mu baratar da kanmu? Allah ne ya tona laifin bayinka, ga mu, mu bayin shugabana ne, da mu da shi wanda aka sami finjalin a wurinsa.”

17. Amma Yusufu ya ce, “Allah ya sawwaƙe mini da in yi haka! Sai shi wanda aka sami finjalin a hannunsa, shi zai zama bawana, amma ku, ku yi tafiyarku lafiya zuwa wurin mahaifinku.”

18. Yahuza ya je wurin Yusufu ya ce, “Ya shugabana, ina roƙonka, ka bar bawanka ya yi magana a kunnuwanka, kada kuma ka bar fushinka ya yi ƙuna bisa bawanka, gama daidai da Fir'auna kake.

19. Ranka ya daɗe, ka tambaye mu, ka ce, ‘Kuna da mahaifi ko ɗan'uwa?’

20. Sai muka amsa, ranka ya daɗe, muka ce, ‘Muna da mahaifi, tsoho, da ɗan tsufansa, auta, wanda ɗan'uwansa ya rasu, shi kaɗai ya ragu daga cikin mahaifiyarsa, mahaifinsa kuwa yana ƙaunarsa.’

21. Sai ka ce wa barorinka, ‘Ku kawo shi wurina, don in gan shi.’

22. Ranka ya daɗe, muka kuwa ce, ‘Saurayin ba zai iya rabuwa da mahaifinsa ba, gama in ya rabu da mahaifinsa, mahaifinsa zai mutu.’

23. Sai ka amsa wa barorinka, ka ce, ‘In ba autanku ya zo tare da ku ba, ba za ku ƙara ganin fuskata ba.’

24. “Sa'ad da muka koma a wurin baranka, mahaifinmu, muka mayar masa da dukan abin da ka ce.

25. Don haka sa'ad da mahaifinmu ya ce, ‘Koma, ku sayo mana ɗan abinci,’

26. sai muka ce, ‘Ba za mu iya gangarawa ba, amma idan autanmu zai tafi tare da mu, za mu gangara, gama ba dama mu ga fuskar mutumin sai ko autanmu yana tare da mu.’

27. Sa'an nan baranka, mahaifinmu, ya ce mana, ‘Kun sani 'ya'ya biyu matata ta haifa mini,

28. ɗayan ya bar ni, na kuwa ɗauka, hakika an yayyage shi kaca kaca, gama ban ƙara ganinsa ba.

29. In kuka ɗauke wannan kuma daga gare ni, mai yiwuwa ne a kashe shi, to, za ku sa baƙin ciki ya ishe ni, da tsufana, har ya kashe ni.’

Karanta cikakken babi Far 44