Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Far 37:5-16 Littafi Mai Tsarki (HAU)

5. Yusufu ya yi mafarki. Sa'ad da ya faɗa wa 'yan'uwansa, suka ƙara ƙin jininsa.

6. Ya ce musu, “Ku ji irin mafarkin da na yi.

7. Ga shi, muna ɗaurin dammuna cikin gona, ga kuwa damina ya tashi tsaye kyam, ga kuma dammunanku suka taru kewaye da shi, suka sunkuya wa damina.”

8. 'Yan'uwansa suka ce masa, “Ashe, lalle ne kai za ka sarauce mu? Ko kuwa, ashe lalle ne kai za ka mallake mu?” Sai suka daɗa ƙin jininsa domin mafarkansa da maganganunsa.

9. Shi kuwa sai ya sāke yin wani mafarki, ya faɗa wa 'yan'uwansa, ya ce, “Ga shi kuma na sāke yin wani mafarki, na ga rana, da wata, da taurari goma sha ɗaya suna sunkuya mini.”

10. Amma sa'ad da ya faɗa wa mahaifinsa da 'yan'uwansa, sai mahaifinsa ya tsauta masa, ya ce, “Wane irin mafarki ne wannan da ka yi? Lalle ne, da ni da mahaifiyarka da 'yan'uwanka za mu sunkuya a gabanka har ƙasa?”

11. 'Yan'uwansa suka ji kishinsa, amma mahaifinsa ya riƙe al'amarin cikin zuciyarsa.

12. Wata rana, da 'yan'uwansa suka tafi kiwon garken mahaifinsu a Shekem,

13. Isra'ila ya ce wa Yusufu, “Ashe, ba 'yan'uwanka suna kiwon garken a Shekem ba? Zo in aike ka wurinsu.”Sai ya ce masa, “Ga ni.”

14. Mahaifinsa ya ce, “Tafi yanzu, ka dubo lafiyar 'yan'uwanka da ta garken, ka kawo mini labarinsu.” Saboda haka, ya aike shi daga kwarin Hebron.Da Yusufu ya isa Shekem,

15. wani mutum ya same shi yana hange-hange cikin karkara. Sai mutumin ya tambaye shi ya ce, “Me kake nema?”

16. Yusufu ya ce, “Ina neman 'yan'uwana ne. Ina roƙonka ka faɗa mini idan ka san inda suke kiwon garkuna.”

Karanta cikakken babi Far 37