Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Far 37:29-34 Littafi Mai Tsarki (HAU)

29. Sa'ad da Ra'ubainu ya koma a wajen rijiya, da bai ga Yusufu a cikin rijiyar ba, sai ya kyakkece tufafinsa,

30. ya koma wurin 'yan'uwansa, ya ce, “Saurayin ba ya nan, ni kuwa, ina zan sa kaina?”

31. Suka ɗauki rigar Yusufu, suka yanka akuya, suka tsoma rigar cikin jinin.

32. Suka kuma ɗauki rigan nan mai ado, suka kawo ta ga mahaifinsu, suka ce, “Ga abar da muka samu, duba ka gani, ta ɗanka ce, ko kuwa?”

33. Da ya gane ita ce, ya ce, “Rigar ɗana ce, wani mugun naman jeji ne ya cinye shi, ba shakka an yayyage Yusufu.”

34. Sai Yakubu ya kyakkece rigunansa, ya yi ɗamara da majayi, ya yi kukan ɗansa har kwanaki masu yawa.

Karanta cikakken babi Far 37