Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Far 37:14-31 Littafi Mai Tsarki (HAU)

14. Mahaifinsa ya ce, “Tafi yanzu, ka dubo lafiyar 'yan'uwanka da ta garken, ka kawo mini labarinsu.” Saboda haka, ya aike shi daga kwarin Hebron.Da Yusufu ya isa Shekem,

15. wani mutum ya same shi yana hange-hange cikin karkara. Sai mutumin ya tambaye shi ya ce, “Me kake nema?”

16. Yusufu ya ce, “Ina neman 'yan'uwana ne. Ina roƙonka ka faɗa mini idan ka san inda suke kiwon garkuna.”

17. Mutumin ya ce, “Sun riga sun tashi daga nan, gama na ji sun ce, ‘Bari mu tafi Dotan.’ ” Saboda haka, Yusufu ya bi sawun 'yan'uwansa, ya kuwa same su a Dotan.

18. Da suka hango shi daga nesa, kafin ya zo kusa da su, sai suka ƙulla su kashe shi.

19. Suka ce wa juna, “Ga mai mafarkin nan can yana zuwa.

20. Ku zo mu kashe shi yanzu, mu jefa shi cikin ɗaya daga cikin rijiyoyin nan, sa'an nan mu ce, wata muguwar dabbar jeji ce ta kashe shi, sa'an nan mu ga yadda mafarkinsa zai zama.”

21. Amma sa'ad da Ra'ubainu ya ji, ya yi ƙoƙari ya cece shi daga hannunsu, yana cewa, “Kada mu raba shi da ransa.

22. Kada mu kashe shi, mu dai jefa shi cikin rijiyan nan a jeji, amma kada mu yi masa lahani.” Ya yi haka da nufin ya cece shi daga hannunsu, ya mayar da shi ga mahaifinsu.

23. Don haka, sa'ad da Yusufu ya zo wurin 'yan'uwansa, suka tuɓe masa rigarsa, rigan nan mai ado wadda take wuyansa.

24. Suka ɗauke shi suka jefa shi cikin rijiyar. Rijiyar kuwa wofi ce, ba ruwa a ciki.

25. Suka zauna su ci abinci, da suka ɗaga ido suka duba, sai ga ayarin Isma'ilawa suna zuwa daga Gileyad, da raƙumansu ɗauke da ƙāro, da man ƙanshi na wartsakewa, da mur, suna gangarawa kan hanyarsu zuwa Masar.

26. Yahuza ya ce wa 'yan'uwansa, “Wace riba ke nan, in mun kashe ɗan'uwanmu, muka ɓoye jininsa?

27. Ku zo mu sayar da shi ga Isma'ilawa, kada mu bar hannunmu ya taɓa shi, gama shi ɗan'uwanmu ne, shi kuma jikinmu ne.” 'Yan'uwansa suka yarda da shi.

28. Da Madayanawa, fatake, suna wucewa, sai suka jawo Yusufu suka fitar da shi daga cikin rijiyar suka sayar wa Isma'ilawa a bakin azurfa ashirin, aka kuwa tafi da Yusufu zuwa Masar.

29. Sa'ad da Ra'ubainu ya koma a wajen rijiya, da bai ga Yusufu a cikin rijiyar ba, sai ya kyakkece tufafinsa,

30. ya koma wurin 'yan'uwansa, ya ce, “Saurayin ba ya nan, ni kuwa, ina zan sa kaina?”

31. Suka ɗauki rigar Yusufu, suka yanka akuya, suka tsoma rigar cikin jinin.

Karanta cikakken babi Far 37