Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Far 27:38-45 Littafi Mai Tsarki (HAU)

38. Sai Isuwa ya ce wa mahaifinsa, “Iyakar albarkar da kake da ita ke nan, baba? Har da ni ma ka sa mini albarka, babana.” Isuwa ya ta da murya ya yi kuka.

39. Sai Ishaku mahaifinsa ya amsa masa ya ce,“Ga shi, ni'imar ƙasar za ta nisancimazauninka,Raɓar samaniya can ƙwanƙoli zata nisance ka.

40. Ta wurin takobinka za ka rayuZa ka yi wa ɗan'uwanka barantaka,Amma sa'ad da ka ɓalle,Za ka kakkarye karkiyarsa dagawuyanka.”

41. Isuwa dai ya ƙi jinin Yakubu saboda albarkar da mahaifinsa ya sa masa. Sai Isuwa ya ce a ransa, “Kwanakin makoki domin mahaifina suna gabatowa, sa'an nan zan kashe Yakubu ɗan'uwana.”

42. Amma maganganun Isuwa babban ɗanta suka kai a kunnen Rifkatu. Saboda haka, sai ta aika aka kirawo Yakubu ƙaramin ɗanta. Ta ce masa, “Ga shi, ɗan'uwanka Isuwa, yana ta'azantar da kansa da nufin ya kashe ka, ya ɗau fansa.

43. Domin haka, ɗana, ka ji muryata, ka tashi ka gudu zuwa wurin Laban ɗan'uwana a Haran,

44. ka zauna tare da shi 'yan kwanaki, har zafin fushin ɗan'uwanka ya huce,

45. ya manta da abin da ka yi masa, sa'an nan zan aika in komo da kai daga can. Don me zan rasa ku, ku biyu a rana ɗaya?”

Karanta cikakken babi Far 27