Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Far 27:34-39 Littafi Mai Tsarki (HAU)

34. Da Isuwa ya ji kalmomin mahaifinsa, sai ya yi kūwwa da kuka mai tsananin gaske, ya ce wa mahaifinsa, “Ka sa mini albarka, har da ni ma, ya babana.”

35. Amma ya ce, “Ɗan'uwanka ya zo cikin makirci, ya karɓe albarkarka.”

36. Isuwa ya ce, “Ba saboda haka ne aka raɗa masa suna Yakubu ba? Gama sau biyu ke nan yake yi mini ƙwace. Ya ƙwace mini matsayina na ɗan fari, ga shi kuma, yanzu ya ƙwace mini albarkata.” Sa'an nan ya ce, “Ba sauran albarkar da ka rage mini?”

37. Ishaku ya amsa wa Isuwa ya ce, “Ga shi, na shugabantar da shi a kanka da dukan 'yan'uwansa na ba shi su, su zama barorinsa, na ba shi hatsi da ruwan inabi. Me zan yi maka kuma, ya ɗana?”

38. Sai Isuwa ya ce wa mahaifinsa, “Iyakar albarkar da kake da ita ke nan, baba? Har da ni ma ka sa mini albarka, babana.” Isuwa ya ta da murya ya yi kuka.

39. Sai Ishaku mahaifinsa ya amsa masa ya ce,“Ga shi, ni'imar ƙasar za ta nisancimazauninka,Raɓar samaniya can ƙwanƙoli zata nisance ka.

Karanta cikakken babi Far 27