Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Far 21:4-16 Littafi Mai Tsarki (HAU)

4. Ibrahim ya yi wa Ishaku ɗansa kaciya yana da kwana takwas, kamar yadda Allah ya umarce shi.

5. Ibrahim kuwa yana da shekara ɗari sa'ad da aka haifa masa ɗansa Ishaku.

6. Saratu ta ce, “Allah ya sa na yi dariya, har dukan wanda ya ji zai yi dariya tare da ni.”

7. Ta kuma ce, “Dā wa zai iya ce wa Ibrahim Saratu za ta bai wa 'ya'ya mama? Duk da haka cikin tsufansa na haifa masa ɗa.”

8. Yaron ya yi girma, aka yaye shi, Ibrahim kuwa ya yi babban biki a ranar da aka yaye Ishaku.

9. Amma Saratu ta ga ɗan Hajaratu Bamasariya wanda ta haifa wa Ibrahim yana wasa da ɗanta Ishaku.

10. Sai ta ce wa Ibrahim, “Ka kori wannan baiwa da ɗanta, gama ɗan baiwan nan ba zai zama magaji tare da ɗana Ishaku ba.”

11. Abin ya ɓata wa Ibrahim zuciya ƙwarai sabili da ɗansa.

12. Amma Allah ya ce wa Ibrahim, “Kada zuciyarka ta ɓaci saboda yaron da kuma baiwarka. Kome Saratu ta faɗa maka, ka yi yadda ta ce, gama ta wurin Ishaku za a riƙa kiran zuriyarka.

13. Zan kuma yi al'umma daga ɗan baiwar, domin shi ma zuriyarka ne.”

14. Ibrahim ya tashi da sassafe, ya kuma ɗauki gurasa da salkar ruwa, ya bai wa Hajaratu, ya ɗora kafaɗarta. Sai ya ba ta ɗanta, ya sallame ta. Ta tafi ta yi ta yawo cikin jejin Biyer-sheba.

15. Sa'ad da ruwan salkar ya ƙare, sai ta yar da yaron a ƙarƙashin wani ƙaramin itace.

16. Sai ta tafi, ta zauna ɗaura da shi da 'yar rata, misalin nisan harbin baka, gama ta ce, “Don kada in ga mutuwar yaron.” Da ta zauna can daura da shi, sai yaron ya ta da muryarsa ya yi ta kuka.

Karanta cikakken babi Far 21