Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Far 13:8-17 Littafi Mai Tsarki (HAU)

8. Abram ya ce wa Lutu, “Kada rashin jituwa ya shiga tsakanina da kai ko tsakanin makiyayanka da nawa, gama mu 'yan'uwa ne.

9. Ba ƙasar duka tana gabanka ba? Sai ka ware daga gare ni. In ka ɗauki hagu in ɗauki dama, in kuwa ka ɗauki dama ni sai in ɗauki hagu.”

10. Lutu ya ɗaga idanunsa sama ya dubi kwarin Urdun, ga shi kuwa da dausayi mai kyau ƙwarai, sai ka ce gonar Ubangiji, kamar ƙasar Masar wajen Zowar, tun kafin Allah ya hallaka Saduma da Gwamrata.

11. Domin haka, Lutu ya zaɓar wa kansa kwarin Urdun duka, Lutu kuma ya kama hanya ya nufi gabas. Haka fa suka rabu da juna.

12. Abram ya zauna a ƙasar Kan'ana, Lutu kuwa ya zauna a biranen kwari, ya zakuɗar da alfarwarsa har zuwa Saduma.

13. Mutanen Saduma kuwa mugaye ne masu aikata zunubi ƙwarai gāba da Ubangiji.

14. Sai Ubangiji ya ce wa Abram, bayan da Lutu ya rabu da shi, “Ɗaga idanunka sama, daga inda kake, ka dubi kusurwoyin nan huɗu,

15. gama dukan ƙasan nan da kake gani kai zan ba, da zuriyarka har abada.

16. Zan mai da zuriyarka kamar turɓayar ƙasa, har in mutum ya iya ƙidaya turɓayar ƙasa, to, a iya ƙidaya zuriyarka.

17. Tashi, ka yi tafiya cikin ratar ƙasar da fāɗinta, gama zan ba ka ita.”

Karanta cikakken babi Far 13