Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Far 13:1-12 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Domin haka Abram ya bar Masar zuwa Negeb, shi da matarsa, da abin da yake da shi duka tare da Lutu.

2. Yanzu Abram ya arzuta da dabbobi, da azurfa, da zinariya.

3. Ya yi ta tafiya daga Negeb har zuwa Betel, har wurin da ya kafa alfarwarsa da fari, tsakanin Betel da Ai,

4. a inda dā ya gina bagade. A can Abram ya kira bisa sunan Ubangiji.

5. Lutu wanda ya tafi tare da Abram, shi kuma yana da garkunan tumaki, da na shanu, da alfarwai,

6. domin haka ƙasar ba ta isa dukansu biyu su zauna tare ba, saboda mallakarsu ta cika yawa, har da ba za su iya zama tare ba.

7. Akwai rashin jituwa kuma a tsakanin makiyayan dabbobin Abram da makiyayan dabbobin Lutu. Mazaunan ƙasar, a lokacin nan Kan'aniyawa da Ferizziyawa ne.

8. Abram ya ce wa Lutu, “Kada rashin jituwa ya shiga tsakanina da kai ko tsakanin makiyayanka da nawa, gama mu 'yan'uwa ne.

9. Ba ƙasar duka tana gabanka ba? Sai ka ware daga gare ni. In ka ɗauki hagu in ɗauki dama, in kuwa ka ɗauki dama ni sai in ɗauki hagu.”

10. Lutu ya ɗaga idanunsa sama ya dubi kwarin Urdun, ga shi kuwa da dausayi mai kyau ƙwarai, sai ka ce gonar Ubangiji, kamar ƙasar Masar wajen Zowar, tun kafin Allah ya hallaka Saduma da Gwamrata.

11. Domin haka, Lutu ya zaɓar wa kansa kwarin Urdun duka, Lutu kuma ya kama hanya ya nufi gabas. Haka fa suka rabu da juna.

12. Abram ya zauna a ƙasar Kan'ana, Lutu kuwa ya zauna a biranen kwari, ya zakuɗar da alfarwarsa har zuwa Saduma.

Karanta cikakken babi Far 13