Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Far 1:3-17 Littafi Mai Tsarki (HAU)

3. Allah ya ce, “Bari haske ya kasance,” sai kuwa ya kasance.

4. Allah ya ga hasken yana da kyau. Allah ya raba tsakanin hasken da duhu,

5. ya ce da hasken, “Yini,” duhu kuwa, “Dare.” Ga maraice, ga safiya, kwana ɗaya ke nan.

6. Allah ya ce, “Bari sarari ya kasance tsakanin ruwaye, don ya raba tsakaninsu.”

7. Allah kuwa ya yi sarari, ya kuma raba tsakanin ruwayen da suke ƙarƙashin sararin da ruwayen da suke birbishin sararin. Haka nan kuwa ya kasance.

8. Allah ya ce da sarari, “Sararin sama.” Ga maraice, ga safiya, kwana na biyu ke nan.

9. Allah kuwa ya ce, “Bari ruwayen da suke ƙarƙashin sararin su tattaru wuri ɗaya, bari kuma sandararriyar ƙasa ta bayyana.” Haka nan kuwa ya kasance.

10. Allah ya ce da sandararriyar ƙasar, “Duniya,” tattaruwan ruwayen da aka tara kuwa, ya ce da su, “Tekuna.” Allah ya ga yana da kyau.

11. Allah kuwa ya ce, “Bari ƙasa ta fid da tsire-tsire, na masu ba da tsaba, da itatuwa masu ba da 'ya'ya, kowanne bisa ga nasa iri, waɗanda suke da 'ya'ya masu ƙwaya a cikinsu, waɗanda irinsa suke cikin duniya.” Haka nan kuwa ya kasance.

12. Ƙasa ta fid da tsire-tsire, na masu ba da 'ya'ya waɗanda suke da ƙwayar irinsu a cikinsu, Allah ya ga yana da kyau.

13. Ga maraice, ga safiya, kwana na uku ke nan.

14. Allah kuwa ya ce, “Bari haskoki su kasance a cikin sararin, su raba tsakanin yini da dare, su kuma zama alamu, da yanayi na shekara, da wokatai.

15. Bari kuma su zama haskoki a cikin sarari su haskaka duniya.” Haka nan kuwa ya kasance.

16. Allah kuwa ya yi manyan haskokin nan biyu, haske mafi girma ya mallaki yini, ƙaramin kuwa ya mallaki dare, ya kuma yi taurarin.

17. Allah ya sa su a cikin sarari su haskaka duniya,

Karanta cikakken babi Far 1