Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Far 1:1-11 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. A sa'ad da Allah ya fara halittar Sama da duniya,

2. duniya ba ta da siffa, sarari ce kawai, duhu kuwa yana lulluɓe da fuskar zurfin teku, Ruhun Allah kuma yana shawagi bisa ruwayen.

3. Allah ya ce, “Bari haske ya kasance,” sai kuwa ya kasance.

4. Allah ya ga hasken yana da kyau. Allah ya raba tsakanin hasken da duhu,

5. ya ce da hasken, “Yini,” duhu kuwa, “Dare.” Ga maraice, ga safiya, kwana ɗaya ke nan.

6. Allah ya ce, “Bari sarari ya kasance tsakanin ruwaye, don ya raba tsakaninsu.”

7. Allah kuwa ya yi sarari, ya kuma raba tsakanin ruwayen da suke ƙarƙashin sararin da ruwayen da suke birbishin sararin. Haka nan kuwa ya kasance.

8. Allah ya ce da sarari, “Sararin sama.” Ga maraice, ga safiya, kwana na biyu ke nan.

9. Allah kuwa ya ce, “Bari ruwayen da suke ƙarƙashin sararin su tattaru wuri ɗaya, bari kuma sandararriyar ƙasa ta bayyana.” Haka nan kuwa ya kasance.

10. Allah ya ce da sandararriyar ƙasar, “Duniya,” tattaruwan ruwayen da aka tara kuwa, ya ce da su, “Tekuna.” Allah ya ga yana da kyau.

11. Allah kuwa ya ce, “Bari ƙasa ta fid da tsire-tsire, na masu ba da tsaba, da itatuwa masu ba da 'ya'ya, kowanne bisa ga nasa iri, waɗanda suke da 'ya'ya masu ƙwaya a cikinsu, waɗanda irinsa suke cikin duniya.” Haka nan kuwa ya kasance.

Karanta cikakken babi Far 1