Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ezra 9:10-14 Littafi Mai Tsarki (HAU)

10. “Yanzu, me za mu ce bayan wannan, ya Allahnmu, gama mun manta da umarnanka.

11. Umarnan da ka umarta ta bakin bayinka annabawa cewa, ‘Ƙasar da kuke shiga don ku mallake ta, ta ƙazantu da ƙazantar al'umman da take cikinta. Ƙazantarsu ta cika dukan ƙasar.

12. Domin haka kada ku aurar musu da 'ya'yanku mata, kada kuma ku auro wa 'ya'yanku 'yan matansu, kada kuma ku nemi zaman arziki da su. Idan kun yi biyayya za ku yi ƙarfi, ku ci albarkar ƙasar, har ku bar ta gādo ga 'ya'yanku har abada.’

13. Bayan wannan dukan abubuwan nan suka same mu saboda mugayen ayyukanmu da zunubanmu masu yawa. Ya Allahnmu, ga shi ma, ka hukunta mu kaɗan bisa ga yawan zunubanmu, ka kuma bar mana wannan ringi.

14. Za mu sake ƙetare umarninka, mu yi aurayya da mutanen da suke yin waɗannan ƙazanta? Ba za ka yi fushi da mu, ka ƙone mu da fushinka har babu ringi ba?

Karanta cikakken babi Ezra 9