Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ezra 8:17-21 Littafi Mai Tsarki (HAU)

17. Na kuma aike su zuwa wurin Iddo, shugaba a Kasifiya. Na faɗa musu abin da za su faɗa wa Iddo a Kasifiya da 'yan'uwansa ma'aikatan Haikali, wato ya aiko mana waɗanda za su yi hidima a Haikalin Allahnmu.

18. Da yake Allah yana tare da mu, sai suka kawo mana mutum mai ganewa daga 'ya'yan Mali ɗan Lawi, ɗan Isra'ila. Sunan mutumin Sherebiya, da 'ya'yansa da 'yan'uwansa, su goma sha takwas ne.

19. Suka kuma kawo Hashabiya tare da Yeshaya daga 'ya'yan Merari. 'Yan'uwansa da 'ya'yansu su ashirin ne.

20. Da kuma ma'aikatan Haikali mutum ɗari biyu da ashirin, waɗanda Dawuda da ma'aikatansa suka keɓe domin su taimaki Lawiyawa. Aka ambaci waɗannan da sunayensu.

21. Na kuma yi shelar azumi a bakin rafin Ahawa don mu ƙasƙantar da kanmu a gaban Allah, mu roƙe shi ya kiyaye mu, da 'ya'yanmu, da kayanmu a hanya.

Karanta cikakken babi Ezra 8