Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ezra 8:1-17 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Waɗannan su ne shugabannin gidajen kakanninsu. Wannan kuwa shi ne lissafin asalin waɗanda suka komo tare da ni daga Babila a zamanin sarautar sarki Artashate.

2-14. Gershom shi ne shugaban iyalin Finehas,Daniyel shi ne na iyalin Itamar,Hattush ɗan Shekaniya, shi ne na iyalin Dawuda.Zakariya shi ne na iyalin Farosh, ya zo da iyalinsa mutum ɗari da hamsin.Eliyehoyenai ɗan Zarahiya, shi ne na iyalin Fahat-mowab, tare da shi kuma akwai mutum ɗari biyu.Shekaniya ɗan Yahaziyel, shi ne na iyalin Zattu, tare da shi akwai mutum ɗari uku.Ebed ɗan Jonatan, shi ne na iyalin Adin, tare da shi akwai mutum hamsin.Yeshaya ɗan Ataliya, shi ne na iyalin Elam, yana tare da mutum saba'in.Zabadiya ɗan Maikel, shi ne na iyalin Shefatiya, yana tare da mutum tamanin.Obadiya ɗan Yehiyel, shi ne na iyalin Yowab, yana tare da mutum ɗari biyu da goma sha takwas.Shelomit ɗan Yosifiya, shi ne na iyalin Bani, yana tare da mutum ɗari da sittin.Zakariya ɗan Bebai, shi ne na iyalin Bebai, yana tare da mutum ashirin da takwas.Yohenan ɗan Hakkatan, shi ne na iyalin Azgad, yana tare da mutum ɗari da goma.Elifelet, da Yehiyel, da Shemaiya, su ne na iyalin Adonikam (su ne suka zo daga baya), suna tare da mutum sittin.Utai da Zabbud, su ne na iyalin Bigwai, suna tare da mutum saba'in.

15. Na kuma tara mutanen a bakin rafin da yake gudu zuwa Ahawa. A nan muka yi zango kwana uku. Sa'ad da na duba jama'a, da firistoci, sai na tarar ba 'ya'yan Lawi.

16. Sai na sa a kirawo Eliyezer, da Ariyel, da Shemaiya, da Elnatan, da Yarib, da Elnatan, da Natan, da Zakariya, da Mehullam waɗanda suke shugabanni, a kuma kirawo Yoyarib da Elnatan masu hikima.

17. Na kuma aike su zuwa wurin Iddo, shugaba a Kasifiya. Na faɗa musu abin da za su faɗa wa Iddo a Kasifiya da 'yan'uwansa ma'aikatan Haikali, wato ya aiko mana waɗanda za su yi hidima a Haikalin Allahnmu.

Karanta cikakken babi Ezra 8