Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ezra 4:2-10 Littafi Mai Tsarki (HAU)

2. sai suka tafi wurin Zarubabel, da shugabannin gidajen kakanni, suka ce musu, “Ku yarda mana mu yi ginin tare, gama muna yi wa Allahnku sujada kamar yadda kuke yi, muna kuma ta miƙa masa sadaka tun kwanakin Esar-haddon, Sarkin Assuriya, wanda ya kawo mu nan.”

3. Amma Zarubabel, da Yeshuwa, da shugabannin gidajen kakannin Isra'ila suka ce musu, “Ba abin da za ku yi tare da mu na ginin Haikalin Allahnmu, amma mu kaɗai za mu yi wa Ubangiji Allah na Isra'ila, gini kamar yadda sarki Sairus, wato Sarkin Farisa, ya umarce mu.”

4. Sai mutanen ƙasar suka shiga karya zuciyar jama'ar Yahuza, su kuwa suka ji tsoron yin gini.

5. Mutanen kuwa suka yi ijara da mashawarta, da za su sa niyyarsu ta shiririce tun daga zamanin Sairus, Sarkin Farisa, har zuwa zamanin Dariyus, Sarkin Farisa.

6. A farkon sarautar Ahasurus, sai suka rubuta takarda ƙara a kan mazaunan Yahuza, da Urushalima.

7. A zamanin Artashate kuma sai Bishlam, da Mitredat, da Tabeyel, da magoya bayansu suka rubuta wa Artashate Sarkin Farisa takarda da harufan Suriya, aka fassara ta.

8. Rehum shugaban sojoji, da Shimshai magatakarda, suka rubuta takardar ƙara a kan Urushalima zuwa Sarki Artashate.

9. Sa'an nan Rehum shugaban sojoji ya rubuta tare da Shimshai magatakarda,da abokansu, da alƙalai, da masu mulkin larduna, da ma'aikatan hukumomi, wato mutanen Farisa, da na Erek, da na Babila, da na Shusha a ƙasar Elam,

10. da sauran al'ummai, waɗanda mai girma, Asnaffar, ya kwaso, ya zaunar da su a biranen Samariya, da sauran wurare na Yammacin Kogi.

Karanta cikakken babi Ezra 4