Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ez 7:7-13 Littafi Mai Tsarki (HAU)

7. Ƙaddararku ta auko muku, ya ku mazaunan ƙasar. Lokaci ya yi, rana ta gabato, ranar tunzuri, ba ta murna da ta sowa a kan duwatsu ba.

8. “Yanzu, ba da jimawa ba, zan fashe hasalata a kanku, in aukar da fushina a kanku, in hukunta ku bisa ga ayyukanku. Zan hukunta ku saboda dukan ƙazantarku.

9. Ba zan yafe ba, ba kuwa zan ji tausayi ba, amma zan hukunta ku bisa ga ayyukanku sa'ad da kuke tsakiyar aikata ƙazantarku, sa'an nan za ku sani ni ne Ubangiji wanda yake hukunta ku.

10. “Ga rana ta zo. Ƙaddararku ta zo, rashin gaskiya ta yi fure, girmankai kuma ya yi toho.

11. Hargitsi ya habaka, ya zama sandan mugunta. Ba wanda zai ragu cikinsu, ko yawaitarsu, ko dukiyarsu, ko wani muhimmi a cikinsu.

12. “Lokaci ya yi, ranar ta gabato, kada mai saye ya yi farin ciki, kada kuma mai sayarwa ya yi baƙin ciki, gama fushina yana kan taron jama'a duka.

13. Mai sayarwa ba zai ta da ciniki ba sa'ad da suke da rai, gama fushina yana bisa kan dukan taron jama'arsu, ba zai fasa ba. Ba wanda yake zamansa cikin zunubi da zai iya shiryar da kansa.”

Karanta cikakken babi Ez 7