Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ez 6:1-10 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ubangiji ya yi magana da ni ya ce,

2. “Ya ɗan mutum, ka zuba ido wajen duwatsun Isra'ila, sa'an nan ka yi annabci a kansu.

3. Ka ce musu, ‘Ya ku duwatsun Isra'ila, ku ji maganar Ubangiji Allah! Haka Ubangiji Allah ya ce a kan duwatsu, da tuddai, da kwazazzabai, da kwaruruka. Ga shi, ni kaina, zan kawo takobi a kanku, zan hallaka wuraren tsafinku.

4. Bagadanku za su zama kango, za a farfasa bagadanku na ƙona turare, zan sa kisassunku su faɗi a gaban gumakansu,

5. zan sa gawawwakin Isra'ilawa a gaban gumakansu, zan warwatsa ƙasusuwanku kewaye da bagadanku.

6. A duk inda kuke zaune, biranenku za su zama kango, wuraren tsafinku da bagadanku za su lalace, gumakanku da bagadanku na ƙona turare za a farfashe su. Za a shafe dukan abin da kuka yi.

7. Za a kashe waɗansu daga cikinku sa'an nan za ku sani ni ne Ubangiji.

8. “‘Duk da haka zan bar waɗansunku da rai, gama waɗansu daga cikinku za su tsere wa takobi, amma zan watsa su cikin sauran al'umma.

9. Waɗansunku da suka tsere za su tuna da ni cikin al'ummai inda aka kai su bautar talala yadda raina ya ɓaci saboda zuciyarsu ta rashin imani wadda ta rabu da ni, da idanunsu masu zina da suke bin gumaka. Za su kuwa ji ƙyamar kansu saboda mugayen abubuwa da suka aikata.

10. Za su kuma sani, ni Ubangiji, ba a banza na ce zan kawo musu wannan masifa ba.”’

Karanta cikakken babi Ez 6