Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ez 48:20-33 Littafi Mai Tsarki (HAU)

20. Dukan yankin da za ku keɓe zai zama murabba'i mai kamu dubu ashirin da dubu biyar [25,000], wato tsattsarkan yankin tare da hurumin birnin.

21. “Ragowar kowane gefe na tsattsarkan yankin da hurumin birnin, zai zama na sarki. Tun daga kamu dubu ashirin da dubu biyar [25,000] na tsattsarkan yankin, zuwa iyakar da take wajen gabas, daga kamu dubu ashirin da dubu biyar [25,000] kuma zuwa iyakar wajen yamma, hannun riga da yankunan kabilan zai zama na sarki. Tsattsarkan yankin da wuri mai tsarki na Haikali za su kasance a tsakiyarsa.

22. Rabon Lawiyawa da hurumin birnin za su kasance a tsakiyar yankin da yake na ɗan sarki. Yankin ɗan sarki zai kasance a tsakanin yankin Yahuza da yankin Biliyaminu.

23. “Sauran kabilan kuwa za su samu. Biliyaminu zai sami yankinsa daga gabas zuwa yamma.

24. Yankin Saminu yana kusa da yankin Biliyaminu daga gabas zuwa yamma.

25. Yankin Issaka yana kusa da yankin Saminu daga gabas zuwa yamma.

26. Yankin Zabaluna yana kusa da yankin Issaka daga gabas zuwa yamma.

27. Yankin Gad yana kusa da yankin Zabaluna daga gabas zuwa yamma.

28. “Kusa da yankin Gad zuwa kudu, iyakar za ta bi ta Tamar zuwa ruwan Meriba-kadesh, sa'an nan ta bi rafin Masar zuwa Bahar Rum.”

29. Ubangiji ya ce, “Wannan ita ce hanyar da za ku raba gādo tsakanin kabilan Isra'ila. Waɗannan kuwa su ne yankunansu, ni Ubangiji Allah na faɗa.”

30. “Ƙofofin birnin a gefen arewa, kamu dubu huɗu da ɗari biyar [4,500] ne.

31. Ƙofofi uku ne, wato Ƙofar Ra'ubainu, da Ƙofar Yahuza, da Ƙofar Lawi. Ana kiran sunayen ƙofofin birnin da sunayen kabilan Isra'ila.

32. A gefen gabas, kamu dubu huɗu ne da ɗari biyar [4,500]. Ƙofofi uku ne, wato Ƙofar Yusufu, da Ƙofar Biliyaminu, da Ƙofar Dan.

33. A gefen kudu, kamu dubu huɗu da ɗari biyar [4,500]. Ƙofofi uku ne, wato Ƙofar Saminu, da Ƙofar Issaka, da Ƙofar Zabaluna.

Karanta cikakken babi Ez 48