Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ez 47:6-15 Littafi Mai Tsarki (HAU)

6. Sai ya tambaye ni, ya ce. “Ɗan mutum, ka ga wannan?”Sa'an nan ya komo da ni zuwa gāɓar kogin.

7. Sa'ad da nake tafiya, sai na ga itatuwa da yawa a kowace gāɓar kogin.

8. Ya kuma ce mini, “Wannan ruwa yana gangarowa zuwa wajen gabas har zuwa cikin Araba. Zai shiga ruwan teku marar gudu, ruwan tekun kuwa zai zama ruwan daɗi.

9. Kowace halitta mai rai da take cikin wannan ruwa za ta rayu. Za a sami kifaye da yawa a ciki, domin wannan ruwa zai kai wurin ruwan tekun, zai kuwa zama ruwan daɗi. Duk inda ruwan nan ya tafi kowane abu zai rayu.

10. Masunta za su tsaya a gāɓar tekun daga En-gedi zuwa En-eglayim. Gāɓar teku za ta zama wurin shanya taruna. Za a sami kifaye iri iri a cikinta kamar kifaye na Bahar Rum.

11. Amma ruwan fadamunsa ba zai yi daɗi ba, za a bar shi a gishirinsa.

12. A kowace gāɓar kogin, itatuwa iri iri na abinci za su yi girma. Ganyayensu ba za su bushe ba, itatuwan kuma ba za su fasa yin 'ya'ya ba, amma su za su yi ta bayarwa a kowane wata, gama ruwansu yana malalowa daga Haikalin. 'Ya'yansu abinci ne, ganyayensu kuwa magani ne.”

13. Ubangiji Allah ya ce, “Waɗannan su ne kan iyaka da za su raba ƙasar gādo ga kabilan Isra'ila goma sha biyu. Yusufu zai sami rabo biyu.

14. Za ku raba daidai, gama na rantse zan ba kakanninku wannan ƙasa, za ta kuwa zama gādonku.

15. “A wajen arewa, iyakar za ta kama daga Bahar Rum, ta bi ta hanyar Hetlon zuwa Zedad,

Karanta cikakken babi Ez 47