Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ez 45:11-23 Littafi Mai Tsarki (HAU)

11. “Kwanon awo na mudu da na garwa girmansu ɗaya ne. Garwa goma ganga guda ne. Ganga ita ce za ta zama fitaccen ma'auni.

12. “Shekel zai zama gera ashirin. Mainanku ɗaya zai zama shekel sittin.”

13. “Wannan ita ce bayarwar da za ku yi. Za ku ba da ɗaya daga cikin shida na mudu daga kowace ganga ta alkama, da ɗaya daga cikin shida na mudu daga kowace ganga ta sha'ir.

14. Za ku ba da ɗaya daga cikin goma ta garwa daga kowace ganga ta mai. Ganga tana cin garwa goma.

15. Za ku ba da tunkiya ɗaya daga kowane garke mai tumaki ɗari biyu, a cikin Isra'ila.“Waɗannan su ne hadayu na gari, da na ƙonawa, da na salama, domin a yi musu kafara, ni Ubangiji Allah na faɗa.

16. “Dukan mutanen ƙasar za su yi wannan bayarwar domin Sarkin Isra'ila.

17. Sarki ne da nawayar ba da hadayun ƙonawa, da na gari, da na sha a lokacin idodi da na amaryar wata, da ranakun Asabar, da lokacin dukan ƙayyadaddun idodin mutanen Isra'ila. Zai kuma ba da hadayu don zunubi da na salama domin a yi wa mutanen Isra'ila kafara.”

18. “Ni Ubangiji Allah na ce, rana ta fari ga watan fari, za ku ɗauki bijimi marar lahani don a tsarkake Haikalin.

19. Firist zai ɗibi jinin hadaya domin zunubi ya shafa shi a madogaran ƙofar Haikalin, da kusurwa huɗu na dakalin bagaden, da ginshiƙan ƙofar fili na can ciki.

20. Za ku yi haka kuma a rana ta bakwai ga watan, saboda wanda ya yi laifi da kuskure, ko da rashin sani. Ta haka ne za ku yi wa Haikalin kafara.

21. “A kan rana ta goma sha huɗu ga watan fari kuma za ku kiyaye Idin Ƙetarewa. Za ku riƙa cin abinci marar yisti har kwana bakwai.

22. A ranar, sarki zai ba da bijimi domin kansa da jama'ar ƙasar, saboda yin hadaya don zunubi.

23. A ranaku bakwai na Idin, zai ba da bijimi bakwai da raguna bakwai marasa lahani hadaya ta ƙonawa ga Ubangiji. Kowace rana kuma zai ba da bunsuru hadaya don zunubi.

Karanta cikakken babi Ez 45