Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ez 44:11-21 Littafi Mai Tsarki (HAU)

11. Za su zama masu hidima a cikin wurina mai tsarki, suna lura da ƙofofin Haikali, suna hidima a cikin Haikalin. Za su yanka hadayar ƙonawa da ta sadaka domin mutane. Za su lura da mutanen, su yi musu hidima.

12. Da yake sun hidimta wa mutane a gaban gumakansu, suka zama sanadin mugun tuntuɓe ga mutanen Isra'ila, don haka ni Ubangiji Allah, na yi rantsuwa cewa za su karɓi hakkin muguntarsu.

13. Ba za su zo kusa da ni a matsayin firistoci don su yi mini hidima ba. Ba za su zo kusa da abubuwana masu tsarki ba, amma za su sha kunya saboda ayyukansu na banƙyama.

14. Amma duk da haka zan sa su lura da Haikalin, su yi dukan hidimomin da za a yi a cikinsa.

15. “Amma Lawiyawan da suke firistoci daga zuriyar Zadok, waɗanda suka lura da Wuri Mai Tsarki sa'ad da mutanen Isra'ila suka karkace, suka bar bina, su ne za su zo kusa da ni, su yi mini hidima, za su kusace ni domin su miƙa hadaya ta kitse da jini, ni Ubangiji Allah na faɗa.

16. Za su shiga Wuri Mai Tsarki, su kusaci teburina, su yi mini hidima, su kuma kiyaye umarnina.

17. Sa'ad da suka shiga ƙofofin fili na can ciki, sai su sa rigunan lilin, kada su sa abin da aka yi shi da ulu, sa'ad da suke hidima a ƙofofin fili na can ciki, da cikin Haikalin.

18. Za su naɗa rawunan lilin, su sa wandunan lilin. Kada su sa abin da zai sa su yi zuffa.

19. Sa'ad da suka fita zuwa filin da yake waje, wurin mutane, sai su tuɓe tufafin da suka yi hidima da su, su ajiye su a tsarkakakkun ɗakuna, sa'an nan su sa waɗansu tufafi domin kada su tsarkake mutane da tsarkakakkun tufafinsu.

20. “Ba za su aske kansu ba, ba kuma za su bar zankayensu su yi tsayi ba, sai su sausaye gashin kansu.

21. Kada firist ya sha ruwan inabi sa'ad da zai shiga fili na can ciki.

Karanta cikakken babi Ez 44