Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ez 44:1-10 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ya kuma komo da ni ƙofar waje ta Haikali wadda take wajen gabas. Ƙofar kuwa tana rufe.

2. Ubangiji ya ce mini, “Wannan ƙofa za ta kasance a rufe, ba za a buɗe ta ba, ba wanda kuma zai shiga ta cikinta, gama Ubangiji Allah na Isra'ila ya shiga ta cikinta, saboda haka za ta kasance a rufe.

3. Sai dai ɗan sarki zai zauna a cikinta ya ci abinci a gaban Ubangiji. Zai shiga ta hanyar shirayin ƙofar, ya kuma fita ta wannan shirayi.”

4. Sa'an nan ya kawo ni a gaban haikalin ta hanyar ƙofar arewa. Da na duba, na ga zatin Ubangiji cike da Haikalin, sai na faɗi rubda ciki.

5. Ubangiji kuwa ya ce mini, “Ɗan mutum, ka lura sosai, ka gani da idanunka, ka kuma ji da kunnuwanka dukan abin da zan faɗa maka a kan dukan ka'idodin Haikalin Ubangiji da dukan dokokinsa. Ka lura sosai da waɗanda aka yardar musu su shiga Haikalin, da waɗanda ba a yarda musu su shiga ba.

6. “Ka ce wa 'yan tawaye, mutanen Isra'ila, ni Ubangiji Allah, na ce, ‘Ku daina ayyukanku na banƙyama.

7. Gama kuna ƙazantar da Haikalina ta wurin shigar da baƙi marasa imani da marasa kaciya, sa'ad da kuke miƙa mini hadayu na kitse da jini. Kun ta da alkawarina da ayyukanku na banƙyama.

8. Ba ku lura da hidimomina masu tsarki ba, amma kuka sa baƙi su lura da wurina mai tsarki.”’

9. Ubangiji Allah ya ce, “Ba wani baƙo marar imani da marar kaciya, daga cikin dukan baƙin da suke cikin jama'ata Isra'ila da zai shiga wurina mai tsarki.

10. “Amma Lawiyawa waɗanda suka yi nisa da ni, suka rabu da ni, suna bin gumakansu, sa'ad da mutanen Isra'ila suka karkata, za su ɗauki alhakin muguntarsu.

Karanta cikakken babi Ez 44