Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ez 42:4-19 Littafi Mai Tsarki (HAU)

4. A gaban ɗakunan akwai hanya mai faɗin kamu goma, tsawonta kuwa kamu ɗari. Ƙofofinsu suna fuskantar arewa.

5. Ɗakunan da suke a hawa na uku ba su da fāɗi, gama hanyar benen ya cinye wuri fiye da ɗakunan da suke a hawa na ƙasa da na tsakiya.

6. Ɗakunan suna da hawa uku, amma ba su da ginshiƙai kamar na farfajiyar da suke waje. Saboda haka ɗakunan da suke a hawa na uku ba su kai girman waɗanda suke a hawa na ƙasa da na tsakiya ba.

7. Tsawon katangar waje wadda take gefen ɗakunan farfajiyar waje wanda yake daura da ɗakunan kamu hamsin ne.

8. Tsawon ɗakunan da suke fuskantar farfajiyar waje kamu hamsin ne. Waɗanda suke fuskantar Haikalin kuwa tsawonsu kamu ɗari ne.

9. Ƙasa da ɗakunan nan akwai ƙofa a gefen gabas, in za a shiga cikinsu daga farfajiyar waje.

10. Akwai kuma ɗakuna a faɗin katangar farfajiyar a wajen gabas a gaban wata farfajiyar da gaban wani gini.

11. Akwai hanya a gaban ɗakunan, sun kuma yi kama da ɗakunan da suke wajen arewa. Tsawonsu, da faɗinsu, da yadda aka shirya su, da ƙofofinsu duk iri ɗaya ne.

12. Kamar ƙofofin ɗakunan da suke wajen kudu, haka nan kuma akwai ƙofa a hanyar da take gaban katanga a wajen gabas, in za a shiga.

13. Sa'an nan ya ce mini, “Ɗakunan da suke wajen kudu da na wajen arewa gaban farfajiya, su ne tsarkakan ɗakuna inda firistoci waɗanda suke kusatar Ubangiji za su ci hadayu mafi tsarki. A nan kuma za su ajiye hadayu mafi tsarki, wato hadaya ta gari, da hadaya domin zunubi, da hadaya domin laifi, gama wurin tsattsarka ne.

14. Sa'ad da firistoci suka shiga Wuri Mai Tsarki, ba za su fita daga cikinsa zuwa farfajiyar da yake waje ba, sai sun tuɓe rigunan aikinsu, gama rigunan tsarkakakku ne. Za su sa waɗansu riguna kafin su tafi inda mutane suke.”

15. Sa'ad da ya gama auna cikin Haikalin, ya fito da ni ta ƙofar gabas, sa'an nan ya auna filin da yake kewaye da Haikalin.

16. Ya auna kusurwar gabas da karan awo, kamu ɗari biyar.

17. Sai kuma ya auna kusurwar arewa, kamu ɗari biyar.

18. Kusurwar kudu kamu ɗari biyar.

19. Kusurwar yamma, ita ma kamu ɗari biyar.

Karanta cikakken babi Ez 42