Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ez 40:12-22 Littafi Mai Tsarki (HAU)

12. Akwai, 'yar katanga a gaban ɗakunan 'yan tsaron, faɗinta kamu ɗaya ne a kowane gefe. Girman ɗakunan 'yan tsaron kuwa kamu shida ne a kowane gefe.

13. Daga bayan rufin ɗaya ɗakin 'yan tsaro zuwa bayan ɗayan rufin ya auna filin ya sami kamu ashirin da biyar.

14. Ya yi ginshiƙai kamu sittin. Akwai ɗakuna kewaye da shirayin da yake bakin ƙofa.

15. Daga gaban ƙofar shiga, zuwa kurewar shirayi na can ciki kamu hamsin ne.

16. Akwai tagogi masu murfi da yake fuskantar ɗakunan 'yan tsaro da kuma ginshikansu waɗanda suke wajen ƙofa a kewaye, haka nan kuma shirayin. Daga ciki kuma akwai tagogi a kewaye. A kowane ginshiƙi an zana siffar itatuwan dabino.

17. Sai ya kawo ni a fili na waje, ga ɗakuna da daɓe kewaye da filin. Akwai ɗakuna talatin a gaban daɓen.

18. Daɓen ya bi ta daidai gefen ƙofofin. Wannan shi ne daɓen da yake ƙasa ƙasa.

19. Sai ya auna nisan da yake tsakanin fuskar ciki ta ƙofar da take ƙasa zuwa fuskar waje ta filin ciki, ya sami kamu ɗari wajen gabas da arewa.

20. Ya kuma auna tsayin ƙofar arewa da faɗinta wadda take fuskantar filin waje.

21. Tana da ɗakuna uku na 'yan tsaro a kowane gefe. Girman ginshiƙanta da shirayinta, daidai suke da ƙofa ta fari. Tsayinta kamu hamsin ne, faɗinta kuwa kamu ashirin da biyar.

22. Girman tagoginta, da na shirayin, da na siffar itatuwan dabinon da aka zana iri ɗaya ne da na ƙofar da ta fuskanci gabas. Tana da matakai bakwai. Shirayinta yana daga can ciki.

Karanta cikakken babi Ez 40