Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ez 37:15-28 Littafi Mai Tsarki (HAU)

15. Ubangiji ya kuma yi magana da ni, ya ce,

16. “Ɗan mutum, ka ɗauki sanda, ka rubuta a kansa, ‘Domin Yahuza da magoyan bayansa.’ Ka kuma ɗauki wani sanda, ka rubuta a kansa, ‘Domin Yusufu, sandan Ifraimu, da dukan mutanen Isra'ila, magoyan bayansa.’

17. Ka haɗa su su zama sanda guda a hannunka.

18. Sa'ad da kuma jama'arka suka ce maka ka nuna musu abin da kake nufi da waɗannan,

19. sai ka faɗa musu, cewa ni Ubangiji Allah na ce zan karɓe sandan Yusufu, wanda yake a hannun Ifraimu da mutanen Isra'ila magoyan bayansa, in haɗa shi da sandan Yahuza in maishe su sanda guda a hannuna.

20. “Sa'ad da sandunan da ka yi rubutu a kansu suna hannunka a gabansu,

21. sai ka faɗa musu, cewa ni Ubangiji Allah na ce, zan komo da jama'ar Isra'ila daga wurin al'ummai inda suka warwatsu, zan tattaro su daga ko'ina, in maido su ƙasarsu.

22. Zan maishe su al'umma guda a ƙasar Isra'ila. Sarki ɗaya zai sarauce su duka, ba za su ƙara zama al'umma biyu ba, ba kuwa za su ƙara zama masarauta biyu ba.

23. Ba za su ƙara ƙazantar da kansu da gumaka da abubuwan banƙyama da kowane irin laifi ba. Zan komo da su daga riddar da suka yi, in tsarkake su. Za su zama jama'ata, ni kuma zan zama Allahnsu.

24. Bawana Dawuda zai sarauce su. Dukansu za su sami shugaba guda. Za su bi ka'idodina su kiyaye dokokina.

25. Za su zauna a ƙasar da kakanninsu suka zauna, wadda na ba bawana Yakubu. Su da 'ya'yansu da jikokin 'ya'yansu za su zauna a can har abada. Bawana Dawuda kuwa zai sarauce su har abada.

26. Zan ƙulla dawwamammen alkawarin salama da su. Zan sa musu albarka, in yawaita su. Zan kafa Haikalina a tsakiyarsu har abada.

27. Wurin Zamana zai kasance a tsakiyarsu, zan zama Allahnsu, su kuma za su zama mutanena.

28. Sa'an nan al'ummai za su sani, ni ne na tsarkake Isra'ila sa'ad da na kafa Haikalina a tsakiyarsu har abada.”

Karanta cikakken babi Ez 37