Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ez 34:11-21 Littafi Mai Tsarki (HAU)

11. “Ni Ubangiji Allah na ce, ni kaina zan nemi tumakina.

12. Kamar yadda makiyayi yakan nemo tumakin da suka watse daga cikin garkensa, haka zan nemi tumakina. Zan cece su daga dukan wuraren da aka watsar da su a ranar gizagizai da baƙin duhu.

13. Zan fito da su daga cikin sauran al'umma, in tattaro su daga ƙasashe dabam dabam, in kawo su ƙasarsu, in yi kiwonsu a kan tuddan Isra'ila, kusa da maɓuɓɓugai, da cikin dukan wuraren da mutane suke zaune a ƙasar.

14. Zan yi kiwonsu a makiyaya mai kyau. Ƙwanƙolin tuddan Isra'ila zai zama wurin kiwonsu. Za su kwanta a makiyaya mai kyau, za su yi kiwo a makiyaya mai dausayi a kan tuddan Isra'ila.

15. Ni kaina zan yi kiwon tumakin, in ba su hutawa, ni Ubangiji Allah na faɗa.

16. “Zan nemo ɓatattu, in komo da waɗanda suka yi makuwa, in ɗora karyayyu, in ƙarfafa marasa ƙarfi, amma zan hallaka ƙarfafan makiyayan nan masu taiɓa, zan hukunta su.

17. “Ni Ubangiji Allah na ce, ‘Ku kuma garkena, zan hukunta tsakanin tunkiya da tunkiya, da tsakanin rago da bunsuru.

18. A ganinku abu mai kyau ne, bayan da kun yi kiwo a makiyaya mai kyau, sa'an nan ku tattake sauran makiyayar da ƙafafunku? Sa'ad da kuka sha ruwa mai kyau, sai kuma ku gurɓata sauran da ƙafafunku?

19. Dole ne tumakina su ci abin da kuka tattake da ƙafafunku, su kuma sha abin da kuka gurɓata da ƙafafunku!’

20. “Saboda haka, ni, Ubangiji Allah, na ce, ‘Zan shara'anta tsakanin turkakkun tumaki da ramammu.

21. Domin kun tunkuɗe marasa ƙarfi da kafaɗunku, kun kuma tunkuye su da ƙahoninku, har kun watsar da su.

Karanta cikakken babi Ez 34