Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ez 31:1-15 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. A kan rana ta fari ga watan uku a shekara ta goma sha ɗaya, Ubangiji ya kuma yi magana da ni, ya ce,

2. “Ɗan mutum, ka ce wa Fir'auna, Sarkin Masar, da jama'arsa.‘Da wa za a kamanta girmanka?

3. Kana kama da Assuriya mai kama da itacen al'ul a Lebanon,Mai rassa masu kyau da inuwar kurmi,Mai tsayi ainun, kansa ya kai cikin gizagizai.

4. Ruwa ya sa ya yi girma,Danshi ya sa ya yi tsayi.Koguna sun gudu kewaye da wurin da aka shuka shi.Yana aikar da rafuffukansa zuwa dukan itatuwan kurmi.

5. Sai ya yi tsayi fiye da dukan itatuwan da suke a kurmi,Rassansa suka yi kauri, suka kuma yi tsayi,Saboda isasshen ruwa a lokacin tohonsa.

6. Dukan tsuntsayen sararin sama sun yi sheƙunansu a rassansa,Namomin jeji kuma suka haifi 'ya'yansu ƙarƙashin rassansa.Dukan al'ummai suka zauna ƙarƙashin inuwarsa.

7. Girmansa yana da kyau, haka kuma dogayen rassansa,Gama saiwoyinsa sun nutse can ƙasa har cikin ruwa.

8. Ko itatuwan al'ul da suke cikin gonar Allah, ba su kai kyansa ba.Itatuwan kasharina kuma ba su kai rassansa ba.Itatuwan durumi kuma ba su kai rassansa ba.Ba wani itace a gonar Allah wanda ya kai kyansa.

9. Na sa shi ya yi kyau, ga kuma rassansa da yawa.Dukan itatuwan Aidan, waɗanda suke cikin gonar Allah sun yi ta jin ƙyashinsa.’

10. Domin haka Ubangiji Allah ya ce, “Saboda ya yi tsayi, kansa kuma ya kai cikin gizagizai, zuciyarsa kuwa ta yi fariya saboda tsayinsa,

11. zan bashe shi a hannun mai ƙarfi, a cikin al'ummai. Zai sāka masa gwargwadon muguntarsa. Na fitar da shi.

12. Baƙi mafi bantsoro daga cikin al'ummai sun sare shi, sun bar shi. Rassansa sun faɗi a kan duwatsun da suke cikin dukan kwaruruka, rassansa kuma sun kakkarye, sun faɗi a cikin dukan magudanan ruwa na ƙasa. Dukan mutanen duniya sun tashi daga inuwarsa, sun bar shi.

13. Dukan tsuntsayen sararin sama za su zauna a gorarsa. Namomin jeji kuma za su yi ta yawo a cikin rassansa.

14. An yi wannan domin kada itatuwan da suke bakin ruwa su yi girma, su yi tsayi da yawa har kawunansu su kai cikin gizagizai, domin kuma kada itacen da yake shan ruwa ya yi tsayi kamarsa, gama an bashe su ga mutuwa zuwa lahira, tare da 'yan adam masu gangarawa zuwa cikin kabari.”

15. Ubangiji Allah ya ce, “A ranar da ya gangara zuwa lahira, na sa zurfi ya rufe shi, ya yi makoki dominsa. Na tsai da kogunansa, yawan ruwansa ya ƙafe. Na sa Lebanon ta yi duhu saboda shi. Dukan itatuwan jeji kuwa sun yi yaushi saboda shi.

Karanta cikakken babi Ez 31