Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ez 28:20-26 Littafi Mai Tsarki (HAU)

20. Ubangiji ya yi magana da ni kuma, ya ce,

21. “Ɗan mutum, ka fuskanci Sidon, ka yi annabci a kanta.

22. Ka ce, Ubangiji Allah ya ce,‘Duba, ina gāba da ke, ya Sidon,Zan bayyana ikona a cikinki,Za su sani ni ne Ubangiji sa'ad da na hukunta ta,Na bayyana tsarkina a cikinta.

23. Zan aukar mata da annoba da jini a titunanta.Waɗanda za a ji musu rauni da takobiZa su fāɗi matattu a tsakiyarta.Za a tasar mata a kowane waje.Sa'an nan za su sani ni ne Ubangiji.’ ”

24. “ ‘A kan mutanen Isra'ila kuwa, al'ummai da suke kewaye da su, waɗanda suka raina su, ba za su ƙara zamar musu kamar sarƙaƙƙiya da ƙaya ba. Sa'an nan za su sani ni ne Ubangiji Allah.’

25. “Ubangiji Allah ya ce, ‘Sa'ad da na tattara mutanen Isra'ila daga cikin sauran al'umma, inda na watsar da su, na kuma bayyana tsarkina a cikinsu a kan idon al'ummai, sa'an nan za su zauna a ƙarsarsu wadda na ba bawana Yakubu.

26. Za su zauna lafiya a cikinta, za su gina gidaje, su yi gonakin inabi. Za su zauna gonakin inabi. Za su zauna lafiya sa'ad da na hukunta maƙwabtansu waɗanda suka wulakanta su. Sa'an nan za su sani ni ne Ubangiji Allahnsu.’ ”

Karanta cikakken babi Ez 28