Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ez 26:12-20 Littafi Mai Tsarki (HAU)

12. Za su washe dukiyarki da kayan cinikinki. Za su kuma rurrushe garunki da kyawawan gidajenki. Za su kwashe duwatsu, da katakai, da tarkace, su zubar a cikin teku.

13. Zan sa a daina raira waƙoƙi da kaɗa garayu.

14. Zan maishe ki fā, wato wurin shanya taruna. Ba za a sāke gina ki ba, ni Ubangiji Allah na faɗa.”

15. Ubangiji Allah ya ce wa Taya, “Sa'ad da kika fāɗi, ƙasashen da suke a gāɓar teku za su girgiza saboda amon fāɗuwarki, da nishin waɗanda ake yi wa rauni, da kashe-kashen da aka yi a cikinki.

16. Sa'an nan sarakunan bakin teku za su sauka daga gadajen sarautarsu, su tuɓe rigunansu, da rigunansu waɗanda aka yi wa ado. Za su zauna a ƙasa suna rawar jiki a kowane lokaci. Za su razana saboda abin da ya same ki.

17. Za su yi makoki saboda ke, su ce,‘Ke wadda ake zaune cikinki, kin bace daga tekuna,Ya shahararren birni, wanda yake babba a bakin teku,Ke da mazaunan da suke cikinki, kun sa mazaunan gāɓar teku su ji tsoro!

18. Yanzu tsibiran za su yi rawar jiki a ranar faɗuwarki.Ji, tsibiran teku za su gigice saboda shuɗewarki.’ ”

19. Gama Ubangiji Allah ya ce, “Sa'ad da na maishe ki kufai kamar biranen da ba a zauna cikinsu ba, sa'ad da kuma na dulmuye ki cikin zurfin teku,

20. sa'an nan zan tura ki tare da waɗanda suke gangarawa zuwa lahira, zuwa wurin mutanen dā. Zan sa ki zauna a ƙarƙashin ƙasa inda ya zama kufai, tare da waɗanda suke gangarawa zuwa lahira, don kada a zauna a cikinki, amma zan ƙawata ƙasar masu rai.

Karanta cikakken babi Ez 26