Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ez 24:8-19 Littafi Mai Tsarki (HAU)

8. Don a tsokani fushina har in yi sakayya,Na zuba jinin da ta zubar a kan dutse,Don kada a rufe shi.’

9. “Saboda haka, ni Ubangiji Allah na ce,‘Kaitonka, ya birni, mai zubar da jini!Ni kuma zan tsiba itace da yawa.

10. Ka tula gumagumai, ka kunna wuta,Ka tafasa naman sosai,Ka zuba kayan yaji a ciki,Ka bar ƙasusuwan su ƙone.

11. Ka ɗora tukunyar da ba kome cikinta a bisa garwashiDomin ta yi zafi, tagullarta ta yi ja wur,Domin dauɗarta ta narke a ciki,Tsatsarta kuma ta ƙone.

12. Ta gajiyar da ni a banza,Wutar ba ta fitar da yawan tsatsarta ba.

13. Ya Urushalima, tsatsarki ita ce ƙazantar lalatarki.Da yake na tsabtace ki, ba ki tsabtatu ba,To, ba za ki ƙara yin tsabta ba,Har lokacin da na fashe fushina a kanki.’

14. Ni, Ubangiji na faɗa, zai tabbata gama zan aikata, ba zan fasa ba, ba kuwa zan ƙyale ba, ba kuma zan bari ba. Zan hukunta ki saboda hanyoyinki da ayyukanki, ni Ubangiji Allah na faɗa ”

15. Ubangiji kuma ya yi magana da ni, ya ce,

16. “Ya ɗan mutum, ga shi, ina gab da ɗauke maka ƙaunatacciyarka farat ɗaya, amma fa, kada ka yi makoki, ko kuka, ko ka zubar da hawaye.

17. Ka yi ajiyar zuciya a hankali, kada ka yi makoki saboda matacciyar. Ka naɗa rawaninka, ka sa takalmanka, kada ka ja amawali, kada kuma ka ci abincin masu makoki.”

18. Sai na yi magana da mutane da safe, da maraice kuwa matata ta rasu. Kashegari da safe, sai na yi kamar yadda aka umarce ni.

19. Mutane kuwa suka tambaye ni dalilin da ya sa nake yin haka.

Karanta cikakken babi Ez 24