Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ez 20:32-48 Littafi Mai Tsarki (HAU)

32. Tunanin nan da kuke yi a zuciyarku, cewa kuna so ku zama kamar sauran al'umma da kabilan ƙasashe, ku bauta wa itace da dutse, ba zai taɓa faruwa ba.’

33. “Hakika, ni Ubangiji Allah na ce, zan sarauce ku ƙarfi da yaji, da fushi,

34. da ƙarfi da yaji da fushi kuma, zan fito da ku daga cikin mutane, in tattaro ku daga sauran ƙasashe inda aka warwatsa ku.

35. Zan kawo ku cikin ruƙuƙin jama'a, in yi muku shari'a fuska da fuska.

36. Kamar yadda na yi wa kakanninku shari'a a jejin ƙasar Masar, haka kuma zan yi muku shari'a, ni Ubangiji Allah na faɗa.

37. “Zan sa ku wuce ta ƙarƙashin sanda, in ƙulla alkawarina da ku.

38. Zan fitar da 'yan tawaye a cikinku, da waɗanda suke yin mini laifi. Zan fito da su daga ƙasar da suke zaune, amma ba za su shiga ƙasar Isra'ila ba. Za ku kuwa sani ni ne Ubangiji Allah.

39. “Ya ku, mutanen Isra'ila, ni Ubangiji Allah, na ce, bari kowa ya tafi ya bauta wa gunkinsa daga yanzu zuwa gaba, tun da yake ba za ku kasa kunne gare ni ba, amma kada ku ɓata sunana mai tsarki da hadayunku da gumakanku.

40. “Gama a kan dutsena ne mai tsarki, wato a bisa ƙwanƙolin dutsen Isra'ila, dukan mutanen Isra'ila za su bauta mini a ƙasar, a nan ne zan karɓe su. A nan kuma zan nemi sadake-sada-kenku, da hadayunku mafi kyau.

41. Zan karɓe ku kamar turare mai ƙanshi sa'ad da na fisshe ku daga cikin sauran mutane, na tattaro ku daga ƙasashen da aka warwatsa ku. Zan nuna tsarkina a cikinku a idon sauran al'umma.

42. Za ku sani ni ne Ubangiji sa'ad da na kawo ku ƙasar Isra'ila, ƙasar da na rantse zan ba kakanninku.

43. A nan za ku tuna da ayyukanku da dukan abubuwa da kuka ɓata kanku da su. Za ku ji ƙyamar kanku saboda mugayen abubuwa da kuka aikata.

44. Za ku sani ni ne Ubangiji sa'ad da na yi muku haka saboda sunana, ba saboda mugayen ayyukanku ba, ya ku mutanen Isra'ila. Ni Ubangiji Allah na faɗa.”

45. Ubangiji ya yi magana da ni ya ce,

46. “Ɗan mutum, ka fuskanci wajen kudu ka ja kunnen mutanen kudu, ka kuma yi annabci gāba da kurmin ƙasar Negeb.

47. Ka ce wa kurmin Negeb, ‘Ka ji maganar Ubangiji, gama Ubangiji Allah ya ce zai kunna wuta a cikinka, za ta kuwa cinye kowane ɗanyen itace, da kowane busasshen itacen da take cikinka. Ba za a kashe harshen wutar ba. Harshen wutar zai babbake kowace fuska daga kudu zuwa arewa.

48. Dukan masu rai za su sani ni Ubangiji ne na kunna wutar, ba wanda zai kashe ta.”’

Karanta cikakken babi Ez 20