Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ez 17:5-10 Littafi Mai Tsarki (HAU)

5. Sai kuma ta ɗauki irin na ƙasar, ta dasa shi a wuri mai dausayi kusa da ruwa mai yawa. Ta dasa shi kamar itacen wardi.

6. Ya yi toho, ya zama kuranga mai yaɗuwa. Rassanta suka tanƙwasa wajenta. Saiwoyinta suka kama ƙasa sosai. Haka ta zama kuranga, ta yi rassa da ganyaye.

7. “ ‘Akwai kuma wata babbar gaggafa mai manyan fikafikai da gashi mai yawa. Sai wannan kuranga ta tanƙwasa saiwoyinta zuwa wajenta, ta kuma miƙe rassanta zuwa wajenta tun daga inda aka dasa ta, don gaggafar ta yi mata banruwa.

8. An dasa ta a wuri mai dausayi inda akwai ruwa da yawa don ta yi ganyaye, ta kuma ba da 'ya'ya, ta zama kurangar inabi ta ƙwarai.’

9. Ka ce, Ubangiji Allah ya ce, ‘Ko wannan kurangar inabi za ta ci gaba? Ashe, gaggafa ta farko ba za ta tumɓuke saiwoyinta, ta sassare rassanta, don ganyayenta da suke tohuwa su bushe ba? Ba sai da hannu mai ƙarfi, ko kuwa da yawan mutane za a tumɓuke ta daga saiwoyinta ba.

10. Idan aka sāke dasa ta kuma za ta yi amfani? Ba za ta bushe sarai sa'ad da iskar gabas ta hura ba? Lalle za ta bushe tun daga inda aka dasa ta ta yi girma.”’

Karanta cikakken babi Ez 17