Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ez 16:38-52 Littafi Mai Tsarki (HAU)

38. Zan hukunta ki kamar yadda akan hukunta mata waɗanda suka ci amanar aure, suka zub da jini. Zan hallaka ki cikin zafin fushina da kishina.

39. Zan bashe ki a hannun kwartayenki, za su kuwa rushe ɗakunan tsafinki, su tuɓe tufafinki, su kwashe murjaninki, su bar ki tsirara tik.

40. “Za su kuta taron mutane a kanki, za su jajjefe ki da duwatsu, su yayanka ki gunduwa gunduwa da takubansu.

41. Za su kuma ƙone gidajenki, su hukunta ki a gaban mata da yawa. Ni kuwa zan sa ki bar karuwanci, ba za ki ƙara ba da kuɗi ga kwartayenki ba.

42. Sa'an nan fushina a kanki zai huce, kishina a kanki zai ƙare. Zan huce, ba zan yi fushi ba kuma.

43. Da yake ba ki tuna da kwanakin kuruciyarki ba, amma kika husatar da ni da waɗannan abubuwa, domin haka zan sāka miki alhakin ayyukanki. Kin yi lalata, banda ayyukanki na banƙyama kuma, ni Ubangiji na faɗa.”

44. Ubangiji ya ce, “Ga shi, duk mai yin amfani da karin magana, zai faɗi wannan karin magana a kanki. ‘Kamar yadda mahaifiya take haka 'yar take.’

45. Ke 'yar mahaifiyarki ce wadda ta ƙi mijinta da 'ya'yanta. Ke kuma 'yar'uwar 'yar'uwanki mata ce waɗanda suka ƙi mazansu da 'ya'yansu. Mahaifiyarki Bahittiya ce, mahaifinki kuwa Ba'amore ne.

46. “'Yarki ita ce Samariya wadda take zaune da 'ya'yanta mata wajen arewa da yake. Ƙanwarki ita ce Saduma wadda take zaune kudu da ke tare da 'ya'yanta mata.

47. Ba ki bi hanyoyinsu da abubuwansu na banƙyama kaɗai ba, sai ka ce wannan ya yi miki kaɗan, amma kin lalace fiye da su.

48. “Hakika ni Ubangiji Allah na ce Saduma ƙanwarki da 'ya'yanta mata ba su yi kamar yadda ke da 'ya'yanki mata kuka yi ba.

49. Wannan shi ne laifin Saduma, ƙanwarki, ita da 'ya'yanta mata, suna da girmankai domin suna da abinci a wadace, suna zama a sangarce, amma ba su taimaki matalauta da masu bukata ba.

50. Su masu alfarma ne, sun aikata abubuwa masu banƙyama a gabana, saboda haka na kawar da su sa'ad da na gani.

51. “Samariya ba ta aikata rabin zunubin da kika aikata ba. Abubuwan banƙyama da kika aikata sun sa 'yan'uwanki sun zama kamar adalai.

52. Ke kuma sai ki sha kunyarki, gama kin sa 'yan'uwanki mata su sami rangwamin shari'a saboda zunubanki da kika aikata fiye da nasu, gama gwamma su da ke. Sai ki ji kunya, ki sha ƙasƙancinki, gama kin sa 'yan'uwanki mata su zama kamar adalai.”

Karanta cikakken babi Ez 16