Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ez 12:10-23 Littafi Mai Tsarki (HAU)

10. Ka ce musu, ni Ubangiji Allah na ce, ‘Wannan jawabi ya shafi shugabannin Urushalima da dukan mutanen Isra'ila, waɗanda suke cikinta.’

11. Ka ce musu, ‘Ni alama ne a gare ku, kamar yadda na yi, haka za a yi da ku, za a kai ku bauta.’

12. Sarkin da yake cikinsu zai ɗauki kayansa ya saɓa a kafaɗarsa, ya fita da duhu. Zai huda katanga ya fita. Zai rufe fuskarsa don kada ya ga ƙasar da idanunsa.

13. Zan yarɓa masa ragata in kama shi. Zan kai shi Babila, wato ƙasar Kaldiyawa, duk da haka ba zai gan ta ba, ko da yake zai rasu a can.

14. Zan warwatsa dukan waɗanda suke kewaye da shi, masu taimakonsa da sojojinsa ko'ina. Zan zare takobi in runtume su.

15. “Sa'an nan za su sani ni ne Ubangiji, sa'ad da na watsa su cikin sauran al'umma da cikin ƙasashe.

16. Amma zan bar kaɗan daga cikinsu su tsere wa takobi, da yunwa, da annoba, don su tuba, su hurta dukan ayyukansu na banƙyama a cikin al'ummai inda suka tafi. Za su sani ni ne Ubangiji.”

17. Ubangiji kuma ya yi magana da ni, ya ce,

18. “Ɗan mutum, ka ci abincinka da rawar jiki, ka sha ruwanka da makyarkyata da damuwa.

19. Ka faɗa wa mutanen ƙasar, cewa ni Ubangiji Allah na ce mutanen Urushalima da suke a ƙasar Isra'ila za su ci abincinsu da razana, su sha ruwansu da tsoro, gama za a washe dukan abin da yake ƙasarsu saboda hargitsin dukan waɗanda suke zaune cikinta.

20. Biranen da ake zaune a cikinsu za su zama kufai, ƙasar kuma za ta zama kango, za su kuwa sani ni ne Ubangiji.”

21. Ubangiji kuma ya yi magana da ni, ya ce,

22. “Ɗan mutum, mene ne wannan karin magana da ake faɗa a ƙasar Isra'ila cewa, ‘Kwanaki suna ta wucewa, wahayi bai gudana ba”?

23. Ka faɗa musu, ka ce ni Ubangiji Allah na ce zan kawo ƙarshen wannan karin magana, ba za su ƙara faɗar wannan karin magana a Isra'ila ba. Amma ka faɗa musu, cewa kwanaki sun gabato da za a tabbatar da kowane wahayi.

Karanta cikakken babi Ez 12