Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ez 11:13-24 Littafi Mai Tsarki (HAU)

13. Sa'ad da nake yin annabci, sai Felatiya ɗan Benaiya, ya rasu. Sai na faɗi rubda ciki na fashe da kuka, na ce, “Ya Ubangiji Allah, za ka ƙare sauran mutanen Isra'ila ƙaƙaf ne?”

14. Ubangiji kuwa ya yi magana da ni, ya ce,

15. “Ɗan mutum, 'yan'uwanka, da danginka, da mutanenka da suke cikin bautar talala tare da kai, da dukan mutanen Isra'ila, su ne waɗanda mazaunan Urushalima suke ce musu, ‘Ku yi nisa da Ubangiji, mu aka mallakar wa wannan ƙasa.’

16. “Domin haka, ka ce, ‘Ni Ubangiji Allah na ce, ko da yake na kai su nesa tsakanin al'ummai, na warwatsa su cikin ƙasashe, duk da haka na zama Haikali a gare su a ɗan lokaci, a ƙasashen da suka tafi.’

17. “Saboda haka ka ce, ‘Ni Ubangiji na ce, zan tattaro ku daga cikin al'ummai, da ƙasashen da aka warwatsa ku, ni kuwa zan ba ku ƙasar Isra'ila.’

18. Sa'ad da suka koma a ƙasar za su kawar da dukan abin da ya ƙazantar da ita, da dukan irin abar ƙyama da take cikinta.

19. Zan ba su zuciya ɗaya, in kuma sa sabon ruhu a cikinsu. Zan kawar musu da zuciya ta dutse, in ba su zuciya mai taushi,

20. domin su kiyaye dokokina, da ka'idodina, su aikata su. Za su zama mutanena, ni kuwa zan zama Allahnsu.

21. Amma waɗanda zuciyarsu ta karkata zuwa ga bin ƙazantattun abubuwa masu banƙyama, zan sāka musu gwargwadon ayyukansu, ni Ubangiji na faɗa.”

22. Sa'an nan kerubobin suka ɗaga fikafikansu tare da ƙafafunsu. Ɗaukakar Ubangiji kuwa tana bisa kansu.

23. Sai ɗaukakar Ubangiji ta bar tsakiyar birni, ta tsaya a bisa kan dutse wanda yake wajen gabas da birnin.

24. Ruhu kuwa ya ɗauke ni a cikin wahayi, ya kai ni Kaldiya wurin 'yan zaman talala. Sa'an nan wahayin da na gani ya rabu da ni.

Karanta cikakken babi Ez 11