Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Esta 6:2-7 Littafi Mai Tsarki (HAU)

2. Sai aka tarar an rubuta yadda Mordekai ya gano maƙarƙashiyar Bigtana da Teresh, biyu daga cikin bābāni na sarki, masu tsaron ƙofa, waɗanda suka yi niyya su kashe sarki Ahasurus.

3. Sai sarki ya ce, “To, wace irin daraja ko girma aka ba Mordekai saboda wannan?”Barorin sarki waɗanda suke yi masa hidima suka ce, “Ba a yi masa kome ba.”

4. Sarki kuwa ya ce, “Wane ne yake a shirayi?”Daidai lokacin ne kuwa Haman ya shigo shirayi na fari na fādar sarki, don ya yi magana da sarki a kan a rataye Mordekai a gungumen itace da ya shirya.

5. Barorin sarki suka ce, “Ai, Haman ne yake tsaye a shirayi.”Sai sarki ya ce ya shigo.

6. Da shigowar Haman, sai sarki ya ce masa, “Me za a yi wa mutumin da sarki yake so ya ɗaukaka?”Haman ya yi tunani ya ce a ransa, “Wane ne sarki yake so ya ɗaukaka, in banda ni?”

7. Sai Haman ya ce wa sarki, “Abin da za a yi wa wanda sarki yake so ya ɗaukaka ke nan.

Karanta cikakken babi Esta 6