Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Esta 3:2-11 Littafi Mai Tsarki (HAU)

2. Dukan barorin sarki waɗanda suke a bakin ƙofar sarki suka rusuna suka yi wa Haman mubaya'a, gama sarki ya umarta a yi masa haka. Amma Mordekai bai rusuna ya yi masa mubaya'a ba.

3. Sai barorin sarki waɗanda suke a bakin ƙofar sarki suka ce wa Mordekai, “Me ya sa ka karya dokar sarki?”

4. Sa'ad da suka yi ta yi masa magana kowace rana, shi kuwa bai kasa kunne gare su ba, sai suka faɗa wa Haman, don su gani ko maganar Mordekai za ta tabbata, gama ya faɗa musu shi Bayahude ne.

5. Sa'ad da Haman ya ga Mordekai bai rusuna ya yi masa mubaya'a ba, sai ya husata.

6. Har ma ya ga a kashe Mordekai kaɗai, wannan bai isa ba. Da yake an faɗa masa asalin Mordekai, sai ya nema ya hallaka dukan Yahudawa, wato kabilar Mordekai, waɗanda suke a dukan mulkin Ahasurus.

7. A watan fari, wato watan Nisan, a shekara ta goma sha biyu ta sarautar sarki Ahasurus, sai suka yi ta jefa Fur, wato kuri'a, a gaban Haman kowace rana da kowane wata har kuri'a ta faɗo a kan watan goma sha biyu, wato watan Adar.

8. Sa'an nan Haman ya ce wa sarki Ahasurus, “Akwai waɗansu mutane da suke warwatse a jama'ar dukan lardunan mulkinka. Dokokinsu sun sha bambam da na sauran mutane, ba su kuma kiyaye dokokin sarki, don haka ba shi da amfani a wurin sarki ya yi ta haƙuri da su.

9. Idan ya gamshi sarki, bari a yi doka a hallaka su, ni kuwa zan ba waɗanda suke tafiyar da aikin sarki, talanti dubu goma (10,000) na azurfa, don su sa a baitulmalin sarki.”

10. Sarki kuwa ya zare zobensa na hatimi daga hannunsa ya ba Haman Ba'agage, ɗan Hammedata, maƙiyin Yahudawa.

11. Sa'an nan ya ce masa, “Da kuɗin, da mutanen duk an ba ka, ka yi yadda ka ga dama da su.”

Karanta cikakken babi Esta 3