Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Esta 2:11-23 Littafi Mai Tsarki (HAU)

11. Kowace rana Mordekai yakan zo shirayin gidan matan kulle don ya san yadda Esta take.

12. Sa'ad da lokacin kowace budurwa ya yi da za ta shiga wurin sarki Ahasurus, bayan da ta riga ta yi wata goma sha biyu na ka'idar yin kwalliyar mata, wato takan shafe jiki da man ƙanshi wata shida, ta kuma shafe jiki da turare da man shafawa wata shida,

13. sa'an nan budurwar za ta shiga wurin sarki, sai a ba ta dukan abin da take bukata ta ɗauko daga gidan matan kullen zuwa fādar sarki.

14. Takan tafi da yamma, ta koma gidan matan kulle na biyu da safe, a hannun Shawashgaz, bābā na sarki, wanda yake lura da ƙwaraƙwarai. Ba za ta ƙara zuwa wurin sarki ba, sai ko ta sami farin jini a wurin sarki sa'an nan a kirawo ta.

15. Sa'ad da lokacin Esta 'yar Abihail, kawun Mordekai, wadda Mordekai ya karɓe ta tankar 'yarsa, ya yi da za ta shiga wurin sarki, ba ta bukaci kome ba, sai dai abin da Hegai, bābā na sarki, wanda yake lura da mata, ya ce. Esta kuwa tana da farin jini a idon duk wanda ya gan ta.

16. Sa'ad da aka kai Esta wurin sarki Ahasurus a fādarsa a wata na goma, wato watan Tebet, a shekara ta bakwai ta sarautarsa,

17. sai sarki ya ƙaunaci Esta fiye da dukan sauran matan. Ta kuwa sami alheri da farin jini a wurinsa fiye da sauran budurwan, saboda haka ya sa kambin sarauta a kanta. Ya naɗa ta sarauniya maimakon Bashti.

18. Sarki kuwa ya yi wa sarakunansa da barorinsa ƙasaitaccen biki saboda Esta. Ya kuma ba larduna hutu, ya ba da kyautai da yawa irin na sarauta.

19. Sa'ad da aka tara budurwai a karo na biyu, Mordekai yana zaune a ƙofar sarki.

20. Har yanzu dai Esta ba ta bayyana asalin danginta da mutanenta ba, kamar yadda Mordekai ya umarce ta, gama Esta tana yi wa Mordekai biyayya kamar ta yi tun lokacin da yake renonta.

21. A kwanakin nan sa'ad da Mordekai yake zaune a ƙofar sarki, sai babani biyu na sarki, wato Bigtana da Teresh waɗanda suke tsaron ƙofar, suka yi fushi, har suka nema su kashe sarki Ahasurus.

22. Wannan maƙarƙashiya ta sanu ga Mordekai, shi kuwa ya faɗa wa sarauniya Esta. Esta kuma ta faɗa wa sarki da sunan Mordekai.

23. Sa'ad da aka bincika al'amarin aka tarar haka yake. Sai aka rataye mutum biyu ɗin a kan gumagumai. Aka kuma rubuta labarin a littafin tarihi a gaban sarki.

Karanta cikakken babi Esta 2