Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Esta 1:15-20 Littafi Mai Tsarki (HAU)

15. Sarki ya ce, “Bisa ga doka, me za a yi da sarauniya Bashti da yake ba ta yi biyayya da umarnin da na aika ta hannun babani ba?”

16. Sai Memukan ya amsa a gaban sarki da sauran sarakai, ya ce, “Ba sarki ne kaɗai sarauniya Bashti ta yi wa laifi ba, amma har dukan sarakai, da sauran jama'a da suke cikin dukan lardunan sarki Ahasurus.

17. Gama za a sanar wa dukan mata abin da sarauniya ta yi, gama abin da ta yi zai sa su raina mazansu, gama za su ce, ‘Sarki Ahasurus ya umarta a kirawo masa sarauniya Bashti, amma ta ki.’

18. Yau ma matan Farisa da Mediya waɗanda suka ji abin da sarauniya ta yi, haka za su faɗa wa dukan hakimai. Wannan zai kawo raini da fushi mai yawa.

19. Idan sarki ya yarda, bari ya yi doka, a kuma rubuta ta cikin dokokin Farisa da Mediya don kada a sāke ta, cewa Bashti ba za ta ƙara zuwa wurin sarki Ahasurus ba. Bari sarki ya ba da matsayinta na sarauta ga wata wadda ta fi ta.

20. Sa'ad da aka ji dokar sarki, wadda zai yi a dukan babbar ƙasarsa, dukan mata za su girmama mazansu, ƙanana da manya.”

Karanta cikakken babi Esta 1