Idan sarki ya yarda, bari ya yi doka, a kuma rubuta ta cikin dokokin Farisa da Mediya don kada a sāke ta, cewa Bashti ba za ta ƙara zuwa wurin sarki Ahasurus ba. Bari sarki ya ba da matsayinta na sarauta ga wata wadda ta fi ta.