Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Dan 9:3-13 Littafi Mai Tsarki (HAU)

3. Sai na mai da hankalina wajen Ubangiji Allah, ina nemansa ta wurin addu'a, da roƙe-roƙe tare da azumi, ina saye da tufafin makoki, na zauna cikin toka.

4. Na yi addu'a ga Ubangiji Allahna, na tuba.Na ce, “Ya Ubangiji, Allah maigirma, mai banrazana, kai mai cika alkawari ne, kana ƙaunar masu ƙaunarka waɗanda suke kiyaye dokokinka.

5. “Mun yi zunubi, mun yi laifi, mun aikata mugunta, mun yi tawaye. Mun kauce daga bin umarnanka da ka'idodinka.

6. Ba mu kasa kunne ga bayinka annabawa ba, waɗanda kuwa suka yi magana da sunanka ga sarakunanmu, da shugabanninmu, da kakanninmu, da dukan jama'ar ƙasa.

7. Ya Ubangiji, kai mai adalci ne, amma mu sai kunya, kamar yadda yake a yau ga mutanen Yahuza, da mazaunan Urushalima da dukan Isra'ilawa, waɗanda suke kusa da waɗanda suke nesa a dukan ƙasashen da ka kora su saboda rashin amincin da suka yi maka.

8. Ya Ubangiji kunya ta rufe mu, mu da sarakunanmu, da shugabanninmu, da kakanninmu, saboda mun yi maka zunubi.

9. Ubangiji Allahnmu mai jinƙai ne mai gafara, amma mu, mun tayar masa.

10. Ba mu yi biyayya ga Ubangiji Allahnmu ta wurin kiyaye dokokinsa ba, waɗanda ya ba mu ta hannun bayinsa annabawa.

11. Dukan Isra'ilawa sun karya dokokinka, sun kauce, sun ƙi bin maganarka. La'ana da rantsuwa waɗanda suke a rubuce cikin dokokin Musa, bawan Allah, sun kama mu domin mun yi maka zunubi.

12. Ya tabbatar da maganarsa wadda ya yi a kanmu da shugabanninmu waɗanda suka yi mulkinmu. Ya aukar mana da babban bala'i, gama a duniya duka ba a taɓa yin irin abin da aka yi wa Urushalima ba.

13. Kamar yadda aka rubuta a dokokin Musa, haka wannan bala'i ya auko a kanmu, duk da haka ba mu nemi jinƙan Ubangiji Allahnmu ba, ba mu daina aikata muguntarmu ba, ba mu lizimci gaskiyarka ba.

Karanta cikakken babi Dan 9