Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Dan 2:17-29 Littafi Mai Tsarki (HAU)

17. Sai Daniyel ya tafi gidansa, ya sanar wa abokansa, wato su Hananiya, da Mishayel, da Azariya da al'amarin.

18. Ya faɗa musu su nemi jinƙai daga wurin Allah na Sama game da wannan matsala, domin kada Daniyel da abokansa su halaka tare da sauran masu hikima a Babila.

19. Sai aka bayyana wa Daniyel asirin ta cikin wahayi da dare. Daga nan Daniyel ya yabi Allah na Sama.

20. Ya ce,“Yabo ya tabbata ga sunan Allah har abada abadin,Wanda hikima da iko nasa ne.

21. Yana da ikon sāke lokatai,Yakan tuɓe sarakuna, ya kuma naɗa waɗansu.Yana ba masu hikima hikima, masu ilimi kuwa fahimi,

22. Yana bayyana zurfafan abubuwa masu wuyar ganewa,Ya san abin da yake cikin duhu.Haske kuma yana zaune tare da shi.

23. A gare ka nake ba da godiya da yabo, ya Allah na kakannina,Gama ka ba ni hikima da iko,Har ka sanar mini da abin da muka roƙe ka,Ka sanar mana da matsalar da ta dami sarki.”

24. Sa'an nan Daniyel ya tafi wurin Ariyok wanda sarki ya sa ya karkashe masu hikima na Babila, ya ce masa, “Kada ka karkashe masu hikima na Babila, ka kai ni gaban sarki, ni kuwa zan yi wa sarki fassarar.”

25. Nan da nan kuwa Ariyok ya kai Daniyel gaban sarki, ya ce masa, “Na sami wani daga cikin kamammun ƙasar Yahuza wanda zai iya sanar wa sarki da fassarar.”

26. Sarki kuwa ya ce wa Daniyel, mai suna Belteshazzar, “Ka iya faɗa mini mafarkin duk da fassararsa?”

27. Daniyel ya amsa wa sarki, ya ce, “Ba masu hikima, ko masu dabo, ko masu sihiri, ko masu duba, da za su iya su warware wa sarki wannan matsala da ta dame shi.

28. Amma akwai Allah a Sama mai bayyana asirai, shi ne ya sanar wa sarki Nebukadnezzar da abin da zai faru a kwanaki masu zuwa. Mafarkinka da wahayinka waɗanda suka zo cikin tunaninka, sa'ad da kake kwance bisa gadonka ke nan.

29. “Ya maigirma, sa'ad da kake kwance a gadonka sai tunanin abin da zai faru nan gaba ya zo maka. Shi kuma wanda yake bayyana asirai ya sanar da kai abin da zai faru nan gaba.

Karanta cikakken babi Dan 2