Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Dan 11:2-9 Littafi Mai Tsarki (HAU)

2. “Yanzu zan faɗa maka gaskiya. Za a ƙara samun sarakuna uku a Farisa, amma na huɗun zai fi dukansu dukiya. Sa'ad da ya ƙasaita saboda dukiyarsa, zai kuta dukan daularsa ta yi gaba da mulkin Hellas.

3. “Sa'an nan wani sarki babba zai taso wanda zai yi mulki da babban iko yadda ya ga dama.

4. Sa'ad da ya ƙasaita mulkinsa zai faɗi, a rarraba shi kashi huɗu a ba waɗansu waɗanda ba zuriyarsa ba, amma ba za su yi mulki da iko kamar yadda ya yi ba, gama za a tumɓuki mulkinsa saboda waɗansu.

5. “Sarkin kudu zai yi ƙarfi, amma ɗaya daga cikin jarumawansa zai ƙasaita fiye da shi, mulkinsa kuma zai zama babba.

6. Bayan waɗansu shekaru za su ƙulla zumunci. Sarkin kudu zai aurar wa sarkin arewa da 'yarsa don sāda zumunci, amma ba za ta sami iko ba. Shi da zuriyarsa ba za su amince da ita ba. Za a yi watsi da ita, ita da masu yi mata hidima, da mahaifinta, da waliyyinta.

7. Ba za a daɗe ba, wani daga cikin danginta zai tasar wa sojojin sarkin arewa da yaƙi, ya shiga kagararsu, ya ci su da yaƙi.

8. Zai kwashe gumakansu ganima, da siffofinsu na zubi, ya kai Masar, tare da tasoshinsu na azurfa da na zinariya masu daraja. Zai yi shekaru bai kai wa sarkin arewa yaƙi ba.

9. Bayan wannan sarkin arewa zai kai wa sarkin kudu yaƙi, amma tilas zai janye, ya koma ƙasarsa.

Karanta cikakken babi Dan 11