Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Dan 10:5-16 Littafi Mai Tsarki (HAU)

5. Da na ɗaga kaina sai na ga wani sāye da rigar lilin, ya ɗaura ɗamara ta zinariya tsantsa.

6. Jikinsa kamar lu'ulu'u yake, fuskarsa kamar walƙiya, idanunsa kuma kamar harshen wuta, hannunwansa da ƙafafunsa kuwa kamar gogaggiyar tagulla, muryarsa kamar ta babban taron jama'a.

7. Ni kaɗai na ga wahayin, gama mutanen da suke tare da ni ba su ga wahayin ba, sai dai babbar razana ta auko musu, har suka gudu, suka ɓuya.

8. Aka bar ni, ni kaɗai, na ga wannan babban wahayi, ni kuwa ba ni da sauran ƙarfi. Fuskata ta sauya, ta turɓune, ba ni da sauran ƙarfi.

9. Sa'an nan na ji muryarsa, da jin muryarsa, sai na faɗi rubda ciki, barci mai nauyi ya kwashe ni.

10. Sai hannu ya taɓa ni, ya tashe ni, sa'an nan hannuwana da gwiwoyina suna ta kaɗuwa.

11. Ya ce mini, “Ya Daniyel, mutumin da ake sonka ƙwarai, ka lura da maganar da zan faɗa maka. Ka miƙe tsaye, gama a wurinka aka aiko ni.” Sa'ad da ya faɗi wannan magana, sai na miƙe tsaye, ina rawar jiki.

12. Sai ya ce mini, “Kada ka ji tsoro, Daniyel, gama tun daga ran da ka fara sa zuciya ga neman ganewa, ka kuma ƙasƙantar da kanka a gaban Allahnka, an ji addu'arka, amsar addu'arka ce ta kawo ni.

13. Shugaban ƙasar Farisa ya tare ni har kwana ashirin da ɗaya, amma Mika'ilu, ɗaya daga cikin shugabanni, ya zo ya taimake ni, ya tsaya wurin sarakunan Farisa.

14. Na zo ne don in ganar da kai a kan abin da zai faru da mutanenka nan gaba, gama wahayin yana a kan kwanaki na nan gaba ne.”

15. Sa'ad da ya faɗa mini wannan magana, na sunkuyar da kaina ƙasa, na yi shiru, ba magana.

16. Sai wani mai kama da ɗan adam ya taɓa leɓunana, sa'an nan na buɗe baki, na yi magana, na ce wa wanda yake tsaye gabana, “Ya shugabana saboda wannan wahayi ciwo ya kama ni, ba ni da sauran ƙarfi.

Karanta cikakken babi Dan 10