Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Dan 10:1-7 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. A shekara ta uku ta sarautar Sairus Sarkin Farisa, sai aka aiko da saƙo wurin Daniyel, wanda aka laƙaba wa suna Belteshazzar. Saƙon kuwa gaskiya ne, ya shafi zancen yaƙi, Daniyel kuwa ya fahimci saƙon.

2. A waɗannan kwanaki, ni Daniyel, ina fama da baƙin ciki har mako uku.

3. A makon nan uku ban ci wani abincin kirki ba, balle nama ko shan ruwan inabi, ban kuma shafa mai ba.

4. A rana ta ashirin da huɗu ga watan fari, ina tsaye a gāɓar babban kogin Taigiris.

5. Da na ɗaga kaina sai na ga wani sāye da rigar lilin, ya ɗaura ɗamara ta zinariya tsantsa.

6. Jikinsa kamar lu'ulu'u yake, fuskarsa kamar walƙiya, idanunsa kuma kamar harshen wuta, hannunwansa da ƙafafunsa kuwa kamar gogaggiyar tagulla, muryarsa kamar ta babban taron jama'a.

7. Ni kaɗai na ga wahayin, gama mutanen da suke tare da ni ba su ga wahayin ba, sai dai babbar razana ta auko musu, har suka gudu, suka ɓuya.

Karanta cikakken babi Dan 10