Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Amos 9:1-8 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Na ga Ubangiji na tsaye a wajen bagade. Ya yi umarni, ya ce,“Bugi ginshiƙan Haikali don shirayiduka yă girgiza.Farfasa su, su fāɗi a kan mutane!Sauran mutane kuwa,Zan kashe su a wurin yaƙi.Ba wanda zai tsere, ko ɗaya.

2. Ko da za su nutsa zuwa lahira,Zan kama su.Ko sun hau Sama,Zan turo su.

3. Ko da za su hau su ɓuya a bisaƙwanƙolin Dutsen Karmel,Zan neme su in cafko su.Ko da za su ɓuya mini a ƙarƙashinteku,Sai in sa dodon ruwa yă yayyage su.

4. Idan kuwa abokan gābansu ne sukakama su,In umarce su su hallaka su datakobi,Tun da na yi ƙudurin ƙare su.”

5. Ubangiji Allah Mai RundunaYa taɓi duniya, ta girgiza.Duk waɗanda suke zaune cikintaSuna baƙin ciki.Duniya duka takan hauTa kuma gangara kamar ruwanKogin Nilu.

6. Ubangiji ya gina al'arshinsa a sama,Ya shimfiɗa samaniya a bisa duniya.Ya sa ruwan teku ya zo,Ya kwarara shi a bisa duniya.Sunansa Ubangiji ne!

7. Ubangiji ya ce, “Jama'ar Isra'ila,Ina yi da ku daidai yadda nake yi daHabashawa.Na fito da Filistiyawa daga Kaftor,Suriyawa kuwa daga Kir,Daidai yadda na fito da ku dagaMasar.

8. Ina dai kallon mulkin nan mai zunubi.Zan hallaka su daga duniya,Amma ba zan hallaka dukan jama'arYakubu ba.

Karanta cikakken babi Amos 9